Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan Yuƙing, ƙaramar jakadiyar ƙasar China dake Legas, ta ce tana kyautata zaton ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙasarta za ta bunƙasa hulɗar kasuwanci da samar da ayyukan yi a Nijeriya.
Madam Yuƙing ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa a Legas cewa hakan zai ƙara haɓaka tunanin samun riba, farin ciki, da tsaron mutanen ƙasashen biyu.
“Muna fatan mu ɗauki taron ƙoli na Beijing da ziyarar Shugaba Tinubu a matsayin wata dama ta zurfafa hadin gwiwa a tsakanin ƙasashenmu a fannonin masana’antu, aikin gona, gina kayayyakin more rayuwa, samar da kuɗaɗe, rage talauci, fasahohin zamani, da sauransu.”
NAN ta ruwaito cewa, taron ƙoli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar China da Afirka, FOCAC, zai gudana ne daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba, a nan birnin Beijing, mai taken “Haɗa Hannu don Ci Gaba da Zamanantar wa da Gina Al’ummar Sin da Afirka tare da Makomar Mai Inganci”
Madam Yuƙing ta ce taron zai yi amfani da takardun sakamako guda biyu, sanarwar da shirin aiwatarwa don samar da babban ra’ayi a tsakanin ɓangarorin biyu, da tsara hanyar aiwatar da haɗin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka cikin shekaru uku masu zuwa.
Ta ce, shugaban ƙasar China , ɗi Jinping, da Tinubu, za su yi nazari kan yadda za a yi haɗin gwiwa tare da tabbatar da ajandar “Sabon Fata” ta Shugaba Tinubu.
