Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE
Wata ƙwararriya a harkar noma da kasuwanci. Zulaihatu Labilwa Madugu, ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su ƙara zuba jari mai yawa a fannin noma, musamman ta hanyar tallafa wa matasa da filayen noma, kayan aiki, da kuma horo na zamani kan harkar.
Zulaihatu ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilinmu a Gombe, inda ta jaddada cewa noma na daga cikin manyan hanyoyin da za su iya rage matsalar rashin aikin yi, fatara, da kuma ƙarancin abinci a ƙasar nan.
Ta ce duk da cewa noma na da wahala, amma sana’a ce mai mutunci wadda ke da matuƙar amfani ga ci gaban tattalin arziki idan aka ba ta kulawar da ta dace.
“Matasa suna da ƙarfi da kuzari da za su iya amfani da su wajen noma idan gwamnati ta ba su dama. Abin da ake buƙata shi ne fili, kayan aiki masu araha, da kuma horo na zamani,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa, idan aka haɗa matasa da fasahar zamani a harkar noma, za su iya samar da wadataccen abinci da kuma ƙara yawan kuɗin shiga ga ƙasa.
Zulaihatu ta kuma buƙaci a samar da hanyoyin tallata amfanin gona bayan girbi, domin rage asarar da manoma ke fuskanta, tare da ƙarfafa su wajen sarrafa amfanin gona maimakon sayar da shi ba tare da ƙarin daraja ba.
A cewarta, idan aka mayar da hankali kan noman matasa, Najeriya za ta samu ci gaba mai ɗorewa a fannin tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
