APC ta fara tantance ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a Zamfara

Spread the love

Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta ƙaddamar da fara tantance yan takarar ta ɓangaren masu neman kujerar majalisar dokokin Jihar a yau Litinin.

Tantancewar yana gudana a Hotel din Karma Guest Inn dake Gusau babban nirnin Jihar.

Masu neman tsayawa takarar sun halarci tantancewar wanda ake gudanar dashi cikin kwanciyar hankali da tsaro.

Wakilin mu ya ruwaito cewar, ana saran a gobe kwamitin tantance yan takarar zai kammala aikin sa.

Da aka tuntuɓe shi, kakakin jam’iyyar ta APC Hon. Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, ya bayyana tantancewar a matsayin cikin kwanciyar hankali, yana mai nuni da cewar za su bada cikakken bayani ga manema labarai bayan kammala tantancewar.

By ukarofi