Sadiya Umar Farouq: Me ya sa ’yan Nijeriya ba sa farin ciki da farautar ta?

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Akasarin ’yan Nijeriya suna da damuwa kan yadda ake wadaƙa da dukiyar ƙasar ba tare da ɗaukar matakan gaske wajen magance matsalar ba, wacce tushenta shine cin hanci da rashawa, wanda ake ganin a matsayin matsalar da ta ƙarya ƙashin-bayan dukkan wani cigaba da bunƙasa a ƙasar. To, amma me ya sa a mafi yawancin lokutan idan gwamnatocin Nijeriya suka fara farautar waɗanda suka riƙe muƙaman gwamnati, kamar Sadiya Umar Farouk, sai ka ga ’yan ƙasar ba su nuna farin ciki da hakan, illa ma sai tir ne ya fi biyo baya?
Manyan misalan a nan sune, tuhumomin da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Duk mai bibiyar lamarin ya san cewa, akasarin talakawan ƙasar sun fi yin suka kan tuhumomin maimakon yabawa, duk da cewa fa hukumomi sun ce suna ƙoƙarin ƙwato dukiyar ƙasa daga hannunsu ne. To, a yanzu ma irin hakan ne yake faruwa da tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouk. Mutane sai sukar hukumar yaƙi da ta’annnatin kuɗi da tattalin arziki (EFCC) suke yi bisa ayyana tsohuwar ministar a matsayin wacce ake nema ruwa a jallo. Shin a ina gizo yake saƙar?

Zance na gaskiya hakan ba ya rasa nasaba da zargin saka siyasa a tuhumar da ake yi wa akasarin ’yan siyasa. Ana bayar da hujja da kasancewar mijin Hajiya Sadiya, wato Air Marshal Sadique Abubakar, tsohon babban hafsan sojojin saman Nijeriya, ya bar Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ya koma jam’iyyar adawa ta ADC, a matsayin dalilin da ya sanya ake tuhumar matar tasa, kamar yadda ake danganta tuhumomin da ake yi wa El-Rufai da Malami kan komawarsu ADC ɗin.

A ranar 9 ga Mayu, 2026, ne hukumar EFCC ta bayar da sanarwar neman Hajiya Sadiya ruwa a jallo bisa tuhume-tuhumen zargin aikata laifuyka guda uku, waɗanda suka haɗa da ‘haɗa baki wajen aikata laifi, saɓa ƙa’idar aiki da karkatar da dukiyar al’umma’.
Ƙarancin yi wa al’umma gamsassun bayanai kan hakan ta hanyar wayar musu da kai, ya sanya hukumomin bincike irin na EFCC sun kasa fita daga zargin da ake yi musu na cewa, akwai ’yan mowa da ’yan bora a cikin waɗanda gwamnati ke tuhuma, inda ake zargin cewa, ainihin laifin da hukumomin suka fi bibiya shine na ƙarfafa jam’iyyar adawa, maimakon na yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, saboda ba a ga an sako waɗanda suka zauna a APC a gaba ba.

Ayar tambayar da mutane suke jefa wa kan tuhumar zargin da ake yi wa Sadiya Umar shine, shin ya aka yi ma tun da fari ta bar Nijeriya ne? Shin ba EFCC ba ce ta ba ta fasfo dinta, don ta fita daga ƙasar neman magani ba ne? Shin kafin ta bar Nijeriya, ta taɓa ƙin amsa gayyatar hukumar? Shin ta taɓa ƙin zuwa ofishin EFCC a duk lokacin da aka buƙaci hakan? Shin an aike mata da gayyatar ta zo a gurfanar da ita a gaban kuliya kafin a ayyana ana neman ta ruwa a jallo ne?
Lallai irin waɗannan tambayoyi suna nan damfare a zukatan ’yan Nijeriya, kuma wajibi ne hukumomi su amsa masu su matuƙar suna so jama’ar ƙasa su gamsu da cewa, ba ’yar zaɓi suke yi wajen tuhumar waɗanda ake zargi ba.

A nan ba wai ana cewa, an wanke tsohuwar ministar daga zargi ba ne ko kuma akasin hakan, a’a, ana so ne a nusar da hukumomin Nijeriya irin kallon da yawancin talakawan ƙasar suke yi musu a duk lokacin da suka yunƙuro wajen tuhumar waɗanda ake zargi. Haƙiƙa warware wannan ƙullin tambayoyi zai matuƙar taimaka wajen dawo da martabar hukumar da kuma kawar da shakku a kanta tare da inganta ayyukanta a idanun al’umma da duniya baki ɗaya.
Dole sai an cire siyasa, alfarma, kusanci, adawa da son zuciya a yaƙin da ake yi na magance aikata almundahana da kuɗaɗen al’umma. Gazawa wajen yin hakan, zai iya sanyawa a ci gaba da wofintar da duk wani yunƙuri da hukumomi suke na yaƙi da cin hanci da rashawa, domin irin su Sadiya za a iya ci gaba da kallon su a matsayin waɗanda badaƙalar siyasa ce kaɗai ta sanya aka hana su sakat a Nijeriya!

Nasir Gwangwazo dan jarida ne mai sharhi kan al’amuran siyasa da na yau da kullum a Nijeriya kuma mazaunin Babban Birnin Tarayya, Abuja

By ukarofi