Yanzu-yanzu: INEC za ta tura ‘yan hidimar ƙasa sama da miliyan 1.4 aikin zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ce za ta ɗauki sama da mutum miliyan 1.4 aikin wucin-gadi domin gudanar da zaɓukan 2027 daga cikin ‘yan hidimar ƙasa na NYSC.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar NYSC a Abuja a yau Litinin.

Ya yaba wa rawar da ‘yan hidimar ƙasar ke takawa wajen gudanar da zaɓukan tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu a Nijeriya.

INEC ta bayyana cewa, za a tura dubban matasa domin gudanar da zaɓukan shugaban kasa, gwamnoni da na ‘yan majalisu, tare da tabbatar da inganta tsaro, inshora da walwalar masu aikin zaɓe a sassan ƙasar.

A cewar Amupitan, NYSC na ɗaya daga cikin ginshiƙan tafiyar da harkokin dimukraɗiyya da ci-gabanta a Nijeriya.

Kazalika, shugaban na INEC ya bayyana cewa a shekarar 2023, hukumar ta ɗauki malaman zaɓe guda miliyan 1.2, waɗanda galibinsu ‘yan NYSC da ɗaliban manyan makarantu ne.

By Babaji