Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bada kyautar sabbin mototoci da yayi alƙawarin ga ɗaliban da suka yi ƙwazo a makarantar kimiya ta KTISM da ke Katsina.
Gwamnan ya miƙa motocin ga ɗaliban a harabar fadar gwamnatin jihar Katsina.
Ɗaliban, Ibrahim Mainasara Bugaje daga sashen Networking and System Security da Aisha Isyaku daga sashen Computer Soft Engineering.
Gwamnan jihar Katsina ya bayyana cewa ya godema Allah da ya bashi ikon cika wannan alƙawarin da ya ɗauka ga ɗaliban tare da masu addu”ar Allah yasa abinda suka karanta ya amfani al’umma.
Shugaban makarantar Dr. Musa Zayyad wanda ya samu wakilcin Hayatu Khalel Bako wanda ya samu rakiyar Librarian Dr. Hindatu Salisu Abubakar, da Bursar Mal Mustapha Abubakar Sadauki, iyayen yaran da dai sauran su.
