Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Sabon Uban ƙasar Shiko Alhaji Garba Zarummai Fana ya bayyana ƙirƙiro masarautu a matsayin wata hanya ta kusantar al’umma ga gwamnati.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja a garin Fana.
Sabon basaraken ya bayyana cewa sanin kowa ne yanzu akwai yawan al’umma saɓanin inda aka fito saboda haka akwai buƙatar al’ummar da a ke jagoranci su kusanci hukumomi tun kama daga masarautu zuwa gwamnati.
Ya kuma yi kira ga hakiman sa da limamai da ke yankin masarautar sa da su ba shi goyon baya domin samun nasara a cikin mulkin sa, haka-zalika su cigaba da biyayya ga shirye-shiryen gwamnati musamman a abinda ya shafi tsaro da kiwon lafiya don samun cigaba mai ɗorewa.
Ya kuma yaba wa masarautar Kabi da gwamna Malam Nasir Idris bisa ga tunanin kusanto da al’umma kusa da su tare da bayar da tabbacin bayar da nasa gudummawa wajen cigaban ƙasa baki ɗaya.
