Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon Sani Aliyu Danlami ya bada kyautar sabuwar mota, babur da maƙudan kuɗaɗe ga ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da ya shirya a mazaɓar sa ta Katsina.
Inda a zagayen ƙarshe ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kangiwa United ta doke abokiyar karawarta da ci biyu da nema wanda hakan ya basu damar lashe kyautar Kofi da sabuwar mota.
Inda na biyun suka samu kyautar sabon mashin ƙirar Bajaj da kudi Naira 500,000, sai waɗanda suka zo na uku sun samu kyautar kuɗi Naira 500,000 sai na huɗu kyautar kuɗi Naira 200,000.
Haka zalika dukkanin ƙungiyoyin da suka fafata a wasan wasu sun samu riguna wasu kuma sun samu ƙwallaye.
Wasan da ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium ya sami halartar jiga jigan ya’yan jam’iyar APC.
