
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar kula da lamuran inganta rayuwar al’umma ta Next Frontiers Hub Initiative (NFHI) ta jagoranci taron tattaunawa da haɗin-gwiwa wanda ya ƙunshi malamai, sarakunan gargajiya da sauran jagororin al’umma da nufin ƙara wa juna sani kan al’amuran da suka shafi ci-gaban al’umma.
An gudanar da taron ne a ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2026 a wani ɗakin taro a Birnin Tarayya Abuja.
A wata sanarwa da Sakatarenta, Ɗahiru Muhammad ya fitar, NFHI ta ce ta taron wani fage ne na tattaunawa, haɗin-gwiwa da bayyana dabaru akan lamuran kuɗi, rage talauci, inganta matasa da kuma harkar ci-gaban ƙasa mai ɗorewa.
Shugabar ƙungiyar, Dakta Fatima Usman Nazir ta samu ganawa da masu ruwa da tsaki musamman a batutuwan da suka shafi kuɗi a Musulunci, inshorar Takaful da cibiyoyin al’ada da nufin faɗaɗa hanyoyin damarmakin haɗaka domin inganta matasa da ƙoƙarin rage talauci acikin al’umma.
Haka kuma, kamfanin inshora na Crown Takaful ya bayar da ceki ga ƙungiyar don bunƙasa harkokinta da kuma ƙoƙarinsa na tasiri acikin al’umma da kula da walwalarsu musamman kan abin da ya shafi lamuran ci-gaban matasa.
NFHI ta kuma jaddada aniyarta ta cigaba da ƙarfafa alaƙa da Crown Takaful da sauran abokan hulɗa wajen aiwatar da shirye-shirye da za su ciyar da harkar inganta matasa gaba, bunƙasa kasuwanci, wayar da kansu kan amfani da kuɗi da kuma walwalar al’umma a sassan Nijeriya.



