Ƙuri’un ‘yan ƙasa za su yi hukunci a zaɓen 2027, inji Amupitan ga Abdulsalam

Spread the love

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Joash Amupitan, ya bayyana cewa ƙuri’un ‘yan Nijeriya za su kasance masu daraja kuma za a tabbatar da sun yi tasiri a babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.

Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ziyarar girmamawa da ya kai wa tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), a gidansa da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.

A yayin ganawar, shugaban INEC ya bayyana Abdulsalami Abubakar a matsayin “uban dimokuraɗiyyar Najeriya”, yana mai yaba irin rawar da tsohon shugaban ƙasar ya taka wajen tabbatar da komawar mulki hannun farar hula a shekarar 1999 da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya a siyasar ƙasar.

Amupitan ya ce INEC za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da cewa zaɓe a Najeriya yana gudana cikin gaskiya, adalci da kuma amincewar jama’a, yana mai jaddada cewa muradin hukumar shi ne ganin kowane ɗan ƙasa ya samu damar bayyana ra’ayinsa ta hanyar ƙuri’a.

Wannan ganawa ta zo ne a lokacin da ake ƙara mayar da hankali kan shirye-shiryen babban zaɓen 2027, inda ake kira ga hukumomin zaɓe da masu ruwa da tsaki su tabbatar da ingantaccen tsari da zai ƙara wa jama’a kwarin gwiwa.

Abdulsalami Abubakar, wanda ke jagorantar Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, na daga cikin manyan mutane da ke taka rawa wajen samar da sulhu da rage rikice-rikicen siyasa a lokutan zaɓe.

Masu bibiyar harkokin siyasa na ganin cewa tabbatar da sahihanci da amincewar jama’a na daga cikin manyan abubuwan da INEC za ta mayar da hankali a kai kafin zaɓen 2027, musamman domin kauce wa matsalolin da kan biyo bayan zaɓuka a baya.

Ganawar Amupitan da Abdulsalami ta kuma nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumar zaɓe, masu ruwa da tsaki da kuma masu fafutukar zaman lafiya domin ganin an gudanar da zaɓe cikin lumana da gaskiya.

By Babaji

Leave a Reply