
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ‘yan fashi sun kai farmaki a Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBU) na yankin Gubi da ke Bauchi a tsakar daren wayewar ranar Litinin, inda suka ƙwace wa ɗalibai wayoyi da wasu kayayyaki masu daraja.
Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kutsa cikin gidan kwanan ɗalibai mata ne da misalin ƙarfe 2 na daren ɗauke da adduna da wuƙaƙe, inda suka riƙa shiga ɗakuna suna yi wa ɗalibai fashi.
Wata shaida da ta nemi a sakaye sunanta, ta ce maharan sun shiga sama da ɗakuna 10 a gidan tare da tserewa da sama da wayoyi 50 da wasu ababe masu daraja na ɗaliban.
Ta bayyana cewa, wasu daga cikin ɗaliban sun samu munanan raunuka, inda wata ta ƙi bayar da wayarta, matakin da ya sa suka sassare ta.
Ta ƙara da cewa, al’amarin ya haddasa tsoro da fargaba acikin ɗalibai kan halin tsaro a yankin Gubi na jami’ar musamman ganin yadda yake da kusanci da ƙauyuka da yankuna masu duhu saboda tarin manyan bishiyu, lamarin da ya sa ayyukan ta’addanci ke da sauƙin aikatawa.
Daraktan yaɗa labaran jami’ar, Zailani Bappa ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce Mataimakin Shugaban Jami’ar (VC), Farfesa Ibrahim Hassan Garba ya ziyarci gidan ɗaliban tare da jajenta musu kan iftila’in.
Haka kuma, ya tabbatar musu da cewa hukumar gudanarwar jami’ar na ƙoƙarin ɗaukar dukkan matakan da suka dace wajen tabbatar da ba wa rayuka da dukiyoyinsu tsaro.
