
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gangamin jam’iyyar APC na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara ya fuskanci ƙalubalen tarzoma, wadda ta yi sanadiyyar raunata magoya baya da dama da kai su asibiti, yayin da ɗan takarar sanata, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya tsallake rijiya da baya a lokacin da aka kai masa farmakin kisa.
Al’amarin ya auku ne a ranar Juma’a, 27 ga Nuwamba, 2026, yayin taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, inda magoya baya masu yawa suka samu munanan raunuka da suka sa aka hanzarta garzayawa da su Babban Asibitin Shinkafi domin kula da lafiyarsu.
Ƙungiyar Wannan Shinkafi Democratic Front ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana kaɗuwarta kan aukuwar lamarin da tasirin da hakan ya yi akan magoya baya da suka halarci taron. Ta ce, Shinkafi, wanda ɗan takarar Sanatan yankin Zamfara ta Arewa ne, ya ziyarci waɗanda suka jikkata a sanadiyyar farmakin, inda ya jajenta musu tare da bayar da tallafin kuɗaɗe a gare su domin biyan kuɗin magani da suke karɓa.
Haka kuma, ya bayar da tallafin N20,000 kowane ɗaya daga cikin marasa lafiyar da ya riska a asibitin ba tare da la’akari da ko suna da alaƙa da gangamin ba. Kazalika, ƙungiyar ta yaba wa ɗan takarar bisa ziyarar tasa ga marasa lafiyar da tallafa musu, inda ta bayyana hakan a matsayin nuna damuwa kan waɗanda tarzoma ta rutsa da su.
Har wa yau, Wannan Shinkafi Democratic Front koka kan yadda aka hargitsa taron na APC, musamman ganin cewa magoya baya da dama sun jikkata da kuma yunƙurin halaka ɗan takarar sanatan, tana mai kria ga hukumomin tsaro da su yi bincike mai zurfi tare da tabbatar da gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu a ciki su fuskanci hukuncin doka.
A ƙarshe, ƙungiyar ta kirayi masu ruwa da tsaki da su a fagen siyasa da magoya baya daga kowace jam’iyya da su yi riƙo da zaman lafiya yayin tarukansu gami da kauce wa dukkan wani abin da zai tayar da zaune-tsaye da ka iya haifar fargabar siyasa a Jihar Zamfara.
