Ɗantasidi ya nuna alhini kan mutuwar masu haƙar ma’adanai 37 a Neja

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Alhaji Abdullahi Dantasidi wato shugaban ƙungiyar haɗin gwiwar masu ƙaramin ƙarfi da na gargajiya ta ƙasa wato (NASSMCS) ya bayyana matsanancin baƙin ciki kan mutuwar masu haƙar ma’adanai 37 a jihar Neja kwanan nan.

Ɗantasidi ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a ƙaramar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa a ranar Lahadi.

A ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026 ne dai jami’an tsaron ma’adinai na hukumar tsaron farin kaya da kare kayayyakin ƙasa (NSCDC) a jihar Neja sun kai samame a wuraren hakar ma’adanai a yankin Wushishi-Lukoto a yammacin Minna babban birnin jihar kuma sun kama mutane da dama da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Sai dai da asubar ranar 17 ga Satumba an tsinci 37 daga cikinsu sun mutu a cikin cunkoson kurkukun NSCDC a Minna.

Da yake magana kan lamarin Ɗantasidi ya bayyana lamarin a matsayin mai raɗaɗi da takaici yana mai cewa rashin masu haƙar ma’adanai ba ƙaramin giba ba ne ga iyalansu kaɗai har ma ga ɓangaren haƙar ma’adanai da Najeriya baki ɗaya.

“Na yi matuƙar kaɗuwa, na yi baƙin ciki da damuwa matuƙa kan wannan lamari. Waɗannan matasa ne da da za su bada gagarumar gudummawa wajen bunƙasar ɓangaren haƙar ma’adanai da cigaban Najeriya amma yanzu babu su,” in ji shi.

Yace yadda ake zargin masu haƙar ma’adanai sun mutu a hannun NSCDC abin damuwa ne, yana buƙatar bincike mai zurfi da kuma buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan fifita tsaro, jin daɗi da muradun masu haƙar ma’adanai a ƙasar saboda a cewarsa, suna bada gagarumar gudummawa wajen bunƙasar ɓangaren haƙar ma’adinan a ƙasar.

“Mu a cikin al’ummar masu hakar ma’adinai na gargajiya mun damu matuƙa da yadda ake mu’amala da mambobinmu kuma muna son hakan ya canza saboda ba tare da masu haƙar ma’adanai na gargajiya da babu wanda zai amfana daga ɓangaren haƙar ma’adinai.

“Duk yadda kake son yiwa wannan ƙungiya laƙabi ba haramtattu ba ne mu, masu haƙar ma’adanai na gargajiya ne kuma muna taimakawa matuƙa wajen cimma manufofin gwamnati a ɓangaren haƙar ma’adinai a wannan ƙasa.

“Masu haƙar ma’adanai na gargajiya sune masu bincike na farko a ɓangaren haƙar ma’adinai. Mu masu zaman kansu ne, masu aiki tuƙuru kuma mun sadaukar da rayuwarmu, mun bar masoyanmu don shiga cikin daji a faɗin ƙasar nan don taimakawa wajen binciko da bayyana inda za a samu albarkatun ma’adanai na ƙasar nan.

“Don haka a yiwa masu haƙar ma’adanai na gargajiya laƙabi da haramtattu a jefa su cikin ƙaramar tantagirarriya kamar masu laifi a bar su su mutu da yawa abin takaici ne. Abin da gwamnati za ta iya yi shi ne ta haɗa kai da wannan ƙungiya don samun moriyar juna,” in ji shi.

Ya kuma yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya da ta samar da abubuwan karfafa gwiwa da za su taimaka wajen ƙara yawan aiki da kuma yawan amfanin masu haƙar ma’adinai na gargajiya la’akari da muhimmiyar rawar da ƙungiyar ke takawa a ɓangaren haƙar ma’adinai.

“Bayan haka ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya fi mayar da hankali kan bangaren haƙar ma’adinai saboda yiwuwar da yake da shi na taimakawa wajen rage talauci a Najeriya matuƙa,” in ji shi.

Ɗantasidi wanda shi ne shugaba kuma babban jami’in zartarwa na rukunin kamfanonin Ɗantasidi, kamfanonin haƙar ma’adanai da saka hannun jari da ke haɗa harkokin haƙar ma’adanai na Asiya da Afirka, mai sha’awa a fannin sarrafa ma’adinai ya kuma jajanta wa gwamnan jihar Neja Umaru Bago da iyalalan mamatan.

Ya kuma buƙaci rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gudanar da bincike mai zurfi kan yadda wannan mummunan lamari ya faru tare da gurfanar da duk waɗanda aka samu da laifi a gaban kuliya.

By ukarofi

Leave a Reply