Ƙaramar Hukumar Jahun ta kashe miliyan N60 don dawo da lantarki

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse

Bayan shafe shekaru takwas cikin duhu da ƙaramar hukumar Jahun tayi na rashin hasken wutar lantarki sakamakon sace kayan wutar lantarki da ɓarayi sukayi a yankin, sabon shugaban ƙaramar hukumar ta Jahun Hon. Jamilu Muhammed Ɗan malam ya kashe kimanin naira miliyan 60 domin ceto al,ummar ƙaramar hukumar daga kwana cikin duhu babu wutar lantarki.

Shugaban ƙaramar hukumar ya faɗi hakane a wata ganawa da ya yi da wakilinmu na Jihar jigawa a ofishinsa da ke Jahun ,ya kuma nuna damuwarsa a kan yadda yanzu wasu unguwanni suke kwana a cikin duhu a garin na jahun.Hakan ya faru ne sakamakon datse wayoyin wutar lantarki ɓarayi suka yi.

Ya ƙara da cewar yanzu haka ƙaramar hukumar ta na nan tana duba yiwuwar sayan wayoyin da waɗannan ɓata gari suka sace domin ganin an samar da hasken wuta a yankunan waɗannan unguwanni.

Ya cigaba da cewar ƙaramar hukumar ta ware Naira miliyan bakwai domin gudanar da wancan aikin wuta da ya jima yana damun al,ummar unguwar bakin caji ofis da unguwar jahun gabas.

Saboda haka ne ma ya shawarci jama,a su sanya ido sosai wajen Kula da kayan da hukuma ta saya domin amfaninsu a matsayin kayan su, Kar su bari wasu marasa kishi su lalata su .

Ya kuma nuna damuwar sa dangane da sace kayan wutar lantarkin da waɗancan ɓatagari su kayi ,yace aƙalla anyi asara da ta kai ta naira Miliyan 70, kuma an sace wayoyin da tsawonsu yakai mita 150 saboda tsadar su ba a samun su sai an je Legas.

Ya kuma koka akan matsalar ƙarancin ruwan sha da ya addabi al,ummar ƙaramar hukumar cikin gari da ƙauyuka sakamakon lalacewar fanfuna masu aiki da hasken rana da kuma tuƙa tuƙa a yankin .

Ya ci gaba da cewar lalacewar fanfunan ya jefa jama, da dama cikin matsalar ƙarancin ruwan sha a garin na Jahun da ƙauyuka.

Ya ƙara da cewar bisa kiyasi fanfuna 19 suka lalace waɗanda ƙaramar hukumar ta ke yin iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta gyara su domin wadata al,umma da ruwan sha.

Domin haka ƙaramar hukumar ta ware Naira miliyan 15 domin tunkarar matsalar ruwan shan.

Shugaban yace, nan bada jimawa ba za a fara gyara fanfuna masu anfani da hasken rana da tuƙa-tuƙa, wanda a faɗin ƙaramar hukumar za ta kashe naira miliyan 20 wajen ganin ta wadata al,ummar ƙaramar hukumar da ruwan sha.

A ɓangaren bayar da tallafi kuma za ta tallafawa matasa da nufin inganta rayuwar al,ummar yankin ta hanyar basu jari da inganta sana’ar su.

By ukarofi