Tsohon Babban Daraktan Tashar Ruwan Nijeriya, Zubairu Ɗambatta ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Babban Daraktan Hukumar Tashar Jiragen ruwa ta Nijeriya (NPA), Alhaji Zubairu AbdulHamid Ɗambatta ya rasu.

Marigayin kuma shi ne mai bada shawara na musamman kan harkar man fetur ga tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo.

Ɗaya daga cikin iyalan gidan marigayin ya shaida wa ‘News Point Nigeria’ cewa, Ɗambatta ya rasu ne a Kano ya na da shekaru 75, bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.

Ya kuma bar mata ɗaya da ƴaƴa dajikoki.

An yi jana’izar mamacin ne a masallacin Usman Bin Affan dake ƙofar Gadon ƙaya, da misalin ƙarfe 1 na rana.

Da fatan Allah Ya jiƙan sa tare da sanya shi a Aljannar Firdausi, Amin.

By Babaji