Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Majalisar ɗinkin duniya ta ware ranar 20 ga watan Nuwanba na kowace shekara a matsayin ranar yara ta duniya.
Yaran da suka fito daga makarantu dadan-daban na Jihar Kano sun jagoranci zaman majalisar dokokin Kano wanda asusun kula da ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya UNICEF reshen jihar Kano ya ɗauki nauyi, taken ranar ta bana shi ne “Kowane yaro yana da yanci”
A yayin zaman majalisar, a ranar Laraba, an gabatar da ƙudirorin da dama waɗanda suka shafi ƙananan yaran da ya shafi ilimi, lafiya, aikin gona da dai sauransu.
Wani yaro mai suna Muhammad Isa shi ne ya jagoranci zaman majalisar a matsayin shugaban majalisar.
Da yake zantawa da Blueprint Manhaja Muhammad Isa ya ce yau wata rana ce da ba zai taɓa mantawa da ita ba, domin ya zauna a kujerar da take da muhimmancin gaske a tsarin mulkin al’umma.
” Ina godewa majalisar ɗinkin duniya da ta ware mana wannan rana a matsayinmu na yara masu tasowa, tabbas wannan rana dole mu yi alfahari da ita sosai”. Inji shugaban majalisar.
Kazalika, wasu daga cikin yaran da suka gudanar da zaman majalisar sun bayyana jin daɗinsu bisa damar da suka samu na zama a zauren majalisar dokokin Jihar Kano albarkacin wannan muhimmiyar rana ta ranar yara ta duniya.
Ko a baya-bayan nan ma a wani taro da hukumar ƙidaya ta Nijeriya ta shirya ta yi hasashen cewa akwai yara sama da miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya wanda yawancinsu sun fiito ne daga yankin Arewa.
A shekarar 1959 MDD ta ayyana ranar 20 ga watan Nuwanba domin bikin yara ta duniya. Sannan a irin ranar ne kuma amma a 1989 majalisar ta samar da dokar ‘yancin yara.
