Daga USMAN KAROFI
A ranar 21 ga Nuwamba, 2024, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta fitar da sammacin kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaro, Yoav Gallant bisa zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza. ICC ta bayyana cewa akwai hujjoji masu ƙarfi da ke nuna Netanyahu da Gallant sun aikata laifukan yaƙi. Kotun ta ce ba lallai ne Isra’ila ta amince da ikon kotun ba kafin gudanar da bincike.
A yayin haka, Amurka ta sake amfani da karfin ikon ta karo na huɗu wajen daƙile ƙudirin kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Wannan mataki ya tabbatar da cewa akwai hannun Amurka a laifukan da aka aikata kan al’ummar Falasɗinawa cikin kwanaki 412 da suka gabata.
A Gaza kaɗai, an kiyasta cewa mutane 43,972 ne suka mutu tare da raunuka 104,008, mafi yawa daga cikinsu yara da mata. Sama da mutane 10,000 sun ɓace ƙarƙashin baraguzan gine-gine. A yankin Yammacin gabar kogin Jordan, ciki har da Gabashin ƙudus sama da Falasɗinawa 700 ne suka rasa rayukansu. Haka kuma mutane 12,000 da suka ji raunuka suna cikin buƙatar a kai su asibitoci domin samun taimakon gaggawa amma Isra’ila ta hana hakan faruwa.
Rahotanni sun bayyana cewa, a Yammacin gabar kogin Jordan, Isra’ila ta tsare mutane 11,700 ciki har da yara 765, mata 435, da ‘yan jarida 58. Daga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu, adadin mutanen da ake tsare da su ya ƙaru daga 5,250 zuwa fiye da 10,000, da yawansu ana tsare da su ba tare da gurfanarwa a kotu ba. A haka mutane biyu sun mutu sakamakon azaba da rashin kula a gidan yari wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu a tsare zuwa 43 cikin watanni 13 da suka gabata.
Cikin wani rahoton UNICEF, ta bayyana cewa yara sama da 14,000 sun mutu a Gaza, yayin da dubban wasu suka ji raunuka. UNICEF ta jaddada cewa babu wani wuri da ke da aminci ga yara a Gaza, kuma dukkan yaran yankin sun fuskanci tsananin wahalar yaƙin. Rahoton Human Rights Watch ya bayyana cewa rushewar gidaje da gine-ginen farar hula a Gaza ba tare da wani dalili ba na iya zama babban laifi bisa tanadin yarjejeniyar Geneva ta 1949.
