
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Mashawarta ta Arewa, ACF, ta dakatar da shugabanta, Mista Mamman Mike Osuman bisa kalamansa na cewa ƴan Arewa za su zaɓi wanda ya zo daga yankin a madadin Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
ACF ta caccaki kalaman shugaban a inda ta ce an fitar da su ne ba tare da yin shawara ba, don haka ba su wakilci matsayar ƙungiyar ba.
Acikin wata takarda da shugaban Tawagar Amintattun ƙungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Ɗalhatu da Sakatarenta, Alhaji Murtala Aliyu suka sanya wa hannu, sun tabbatar da cewa, Mista Osuman ya faɗi kalaman ne waɗanda ke wakiltar ra’ayin kai-da-kai wanda kuma yin hakan laifi ne a tsarin tafiyar da ƙungiyar.
Saboda haka ne Tawagar Amintattun da Majalisarta ta Zartarwar suka tabbatar da dakatar da Mista Osuman da kuma samar da kwamiti da zai yi bincike game da lamarin.
