Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa ta ɗauki matakan magance matsalolin lantarki a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A taronta karo na 146, Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa, NEC ta ƙudiri aniyar haɓaka sabbin dabarun hana faɗuwar turakun wutar lantarki da ake fuskanta a Nijeriya.

Majalisar, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta fitar da jaddawalin shawarwarin da suka haɗa da samar da wani kwamitin bibiyar gyaran wutar a mataki na ƙasa, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Jihar Cross-River, Bassey Otu.

Wata takarda da Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin rediyon da yaɗa labarai ta ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Rahama Abdulmajid ta fitar, ta ce sabon kwamitin zai mayar da hankali ne wajen tuntuɓar jihohi da sanya ido kan ganin an aiwatar da dokar sake fasalin wutar lantarki ta 2023 wadda gwamnati ta amince da ita.

Ta kuma ce hukumar ta kuma jaddada buƙatar yin garambawul ga tsarin rarraba wutar, ta yadda za a bai wa jihohi damar samar da wutar lantarki mai sauƙi ga yankunansu.

Mataimakin shugaban ƙasar, ya nanata cewa samar da wadataccen makamashi haƙƙi ne da ya rataya a wuyan gwamnati da kasancewarsa ƙahon zuciyar tattalin arziƙi.

Majalisar ta kuma buƙaci jihohi da su sanya hannu a cikin shirin samar da shiyoyin ma’aikatun sarrafa kayan noma na Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ), wanda ke da nufin bunƙasa noma da masana’antu.

Kazalika, hukumar ta amince da naɗin mutanen da za su yi aiki a majalisar gudanarwa ta hukumar saka hannun jari ta ƙasa, wato (NSIA).

Majalisar ta rufe zaman nata da bayar da umarni ga Hukumar Kula da Ababen More rayuwa ta Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa (NASENI) da ta gyara taraktoci da sauran injinan noma tare da haɓaka kafa masana’antar batirin lithium.

By Babaji