Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Makonni bayan miƙa wasu ƙudurori huɗu da ke da nufin yin garambawul ga tsarin harajin Nijeriya ga majalisar mokokin ƙasar da Shugaba Bola Tinubu ya yi, har yanzu wannan batu na ci gaba da haifar da cecekuce a majalisar da ma ɓangarorin ƙasar baki ɗaya game da manufar waɗannan ƙudirorin.
Wasu dai sun bayyana fargabar cewa ƙudurorin na iya jawo ƙarin haraji ta yadda za su ƙara ɗora wa ‘yan ƙasar nauyi.
Ra’ayoyin ‘yan Nijeriya dai sun bambanta kan wannan lamari, inda da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan abin da wannan ƙuduri ke nufi, amma wasu kuma sun zaɓi su jira cikakken bayani kafin su yi tsokaci a kai.
Amma babban abin da ya fi ci wa talakan Nijeriya tuwo a ƙwarya shi ne: ta yaya waɗannan sauye-sauyen za su shafi rayuwarsu?
Haraji kan kuɗaɗen da mutane ke samu:
ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo cece-kuce a ƙudirin dokar shine batun harajin da ake cirewa daga kuɗin da mutum ke samu, wato ‘Personal Income Taɗ’ a turance.
A sabon ƙudirin dokar, an sake fasalin harajin da ake cirewa daga aljihun jama’a, inda Gwamnatin Tarayya ta yi iƙirarin cewa za a ɗauke nauyin haraji daga kan masu ƙaramin ƙarfi.
ƙudirin dokar ya ce, ba za a buƙaci mutanen da ke samun kuɗaɗen da suka yi ƙasa da Naira 800,000 a shekara su biya haraji kan waɗannan kuɗaɗen ba, har sai kuɗn da ake samu a shekara ya kai miliyan 2.2 kafin ya fara biyan harajin kashi 15 cikin 100 a kai.
A wani ɓangaren kuma, dokar ta ƙara kason harajin da waɗanda kuɗadensu suka zarta wannan adadin za su biya, kamar yadda Dr Zaid Abubakar, shugaban hukumar tattara kuɗaden shiga ta jihar Kano ya yi bayani.
”Harajin an yi shi ne kamar yadda ake cewa a Turance ‘progressiɓe’, ma’ana yayin da kuɗin da kake samu ke ƙaruwa haka ma kason harajin da kake biya ke ƙara yawa, amma da gaske masu ƙaramin ƙarfi za su samu sauki ta wannan ɓangaren”.
Dr Zaid ya ƙara da cewa, a wani ɓanagren kuma wannan dokar na iya sanya mutane su fara ɓoye asalin kuɗaɗen da suke samu domin su guje wa biyan haraji a kai.
“Ganin haka, ba kowa ne zai iya bayyana ainihin kuɗin da yake samu ba, wasu za su fara ɓoye-ɓoye, suna rage kuɗin da suke samu a shekara, sai dai idan gwamnati ba ta ɓullo da wata hanyar gano irin waɗannan bayanan ba, wannan na ɗaya daga cikin illolin da dokar za ta iya haifarwa” in ji shi.
Harajin ɓAT:
Wataƙila ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke cikin tanade-tanade da yawa na wannan ƙuduri shi ne abin da ya shafi harajin ɓAT, wanda shi ne harajin da ake sanyawa a kan kayayyakin da aka sarrafa.
Gwamnatin Nijeriya ta yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ya saurari koke-koke da ‘yan Nijeriya ke yi, musamman talakawan ƙasar waɗanda ke fama da matsalar tsadar rayuwa sakamakon manufofin gwamnatin na gyara tattalin arzikin ƙasar, wanda ya sa dokar ta bayar da damar cire harajin ɓAT a kan kayayyakin abinci, kayayyakin asibiti, da Ilimi, da kasuwancin sufuri.
Misali; kuɗin makaranta ko hayar da masu gida ke biya ko siyayyar da masu makaranta suka yi don kasuwancin ilimantar da ‘yan Nijeriya ba za su kasance daga cikin waɗanda ake biyan harajin ɓAT akansu ba. Haka abin yake ga masu asibitoci, da masu sana’ar noma, da masu siyan ababen hawa na sufuri.
Amma dokar ta ce za a ƙara kason da ake karɓa a matsayin ɓAT daga kashi 7.5 cikin ɗari zuwa kashi 15, wanda hakan kamar yadda Dr Zaid ya yi bayani yana iya ƙara farashin kayayyakin da ‘yan Nijeriya ke saya a kasuwa sakamakon ƙarin harajin da masu sarrafa kayayyakin za su fuskanta.
Ya ce, “duk abin da ake biyan harajin a kai yana iya ƙara kuɗi, manyan misaial giuda biyu su ne kuɗin wutar lantarki da kuma amfani wayar salula, mutane za su rage watyar da suke bugawa kuma har farashin data ma zai ƙaru wanda hakan na iya kawo cikas a rayuwar mutane.”
Dr Zaid ya ƙara da cewa, idan aka ƙara farashin lantarki, dole ne kamfanoni masu sarrafa kaya su ƙara farashin kayayyakinsu wanda daga ƙarshe ‘yan Nijeriya ne za su cike giɓin da aka samu a ribar da kamfanoni ke nema kan kayayyakinsu.
Makomar kaso da biyan harajin ɓAT ga jihohi:
Wani babban abu da ya fi jan hankali a batun sababbin ƙudirorin harajin shine, yadda za a kasa da biyan kuɗin harajin kayayyaki na ɓAT a Nijeriya. A yayin da akasarin mutane ke cewa, jihohi irin su Legas za su fi morar wannan sabon tsari, amma Shugaban Kwamitin Fadar Shugaban ƙasa Sauya Fasalin Haraji, Taiwo Oyedele, ya yi ƙarin haske da cewa, an gabatar da sabon fasalin biyan harajin ne, saboda a bai wa kowacce jiha haƙƙinta daidai gwargwado ba tare da fifita wata jiha ba.
A cewarsa, rabon harajin kayan masarufi da ake amfani da shi a halin yanzu ya nemi a riƙa biyan hedikwatar kamfani ko masana’antar da aka sarrafa ko samar da kayan ne ba tare da la’akari da jihar da aka yi amfani da kayan ba, yana mai cewa, a sabon ƙudiirin dokar za a fifita jihar da aka yi amfani da kaya ne kawai.
Ya yi dalla-dalla da cewa, “a tsarin da ake amfani da shi yanzu na rabon harajin kayayyaki a na kasafta harajin ne kamar haka; kashi 15 ga Gwamnatin Tarayya, kashi 50 ga jihohi da Babban Birnin Tarayya, sai kuma kashi 35 ga ƙananan hukumomi.
“Amma sabon ƙudirin da aka gabatar zai rage yawan kason Gwamnatin Tarayya ta hanyar biyan haraji ga jihar da aka yi amfani da kaya.”
Bayanin Mista Oyedele ya yi nuni da cewa, maimakon misalin Jihar Legas da ke kwashe akasarin harajin da ake amsa a halin yanzu sakamakon yawancin kamfanoni da masana’antu da bankunan ƙasar suna da hedikwata a Legas, duk da cewa, ba a Legas ake amfani da kayayyakin da suke sarrafawa ba, yanzu za a biya haraji ne ga duk jihar da aka yi amfani da kayan ne.
Harajin bunƙasa ayyukan cigaba:
Batun harajin da ake amfani da shi domin bunƙasa ayyukan da ke kawo ci gaba a al’umma wanda aka fi sani da ‘Deɓelopment Leɓy’ wanda shi ne ake amfani da shi wurin gudanar da ayyuka da shirye-shirye na wasu hukumomin gwamnati da suka haɗa da asusun tallafawa ɓangaren ilimi (TETFUND) da hukumar kula da ci gaban fasahar sadarwa (NITDA) da kuma hukumar inganta ɓangaren kimiyyar injiniyoyi (NASENI).
Sabuwar dokar za ta nemi a rage kuɗaɗen da ake bai wa waɗannan hukumomi daga shekara ta 2025 zuwa shekara ta 2030 inda za a dakatar da ba su duk wasu kuɗaɗe. hakan na iya gurgunta ayyukan da waɗannan hukumomi ke gudanarwa wanda suka shafi ɓangarorin ilimi da kimiyya wanda ke matuƙar tasiri a rayuwan ‘yan Nijeriya baki ɗaya.
Farfesa Ahmed Bello Dogarawa malami ne a tsangayar nazarin akanta da ke jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya bayyan cewa dokar za ta buƙaci a mayara da harajin da ake bai wa waɗannan hukumomi ya zama guda ɗaya a madadin yadda ya ke a yanzu da kowace hukuma tana da na ta.
”Za a mayar da harajin ya zama guda ɗaya a tsakanin waɗannan hukumomin, amma inda matsalar ita ce a wurin rabo. Ttsakanin shekarar 2025 zuwa 2027 idan aka karɓi wannan harajin za a riƙa bai wa hukumar TETFUND kashi 50 kowace shekara, sannan a 2027 za a dakatar da bai wa NITDA da NASENI ko kwabo, ba su da wata hanya da za su samu kuɗin gudanar da al’amuransu.
“Daga shekara ta 2030, ita ma TETFUND za a dakatar da kuɗaɗen da ake ba ta, kuma za a fara amfani da duka kuɗin da aka samu wurin bai wa ɗalibai bashi.”
A halin da ake ciki yanzu dai ba a cimma matsaya kan waɗannan sauye-sauyen da ake neman yi a ɓangaren harajin ƙasar ba, yayin da ƙudirorin ke gaban majalisun dattawa da ta wakilai.
Rufewa:
Lallai akwai buƙatar a fito da wannan ƙudirin doka bainar jama’a, domin nazari akanta dalla-dalla ta yadda al’umma za su fahimce ta, domin akasarin bayanan da fito fara fitowa fili su na barazana ne ga wasu ɓangarori na ƙasar, musamman yankin Arewa, wanda ke kallon ƙudirin a matsayin koma-baya gare shi, kamar yadda ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) da ƙungiyar Gwamnonin Arewa suka koka, har ma da yadda Majalisar Tattalin Arziki ta Nijeriya, wacce ta ƙunshi dukkan gwamnonin ƙasar da sauran masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban ƙasa Kashin Shettima ita ma majalisar ta nemi da a dakatar da ƙudirin har sai bayan an yi cikakkiyar tuntuɓa a faɗin ƙasar.
