
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta jinjina wa Rundunar sojojin sama bisa namijin ƙoƙari da suka yi wajen daƙushe ƴan ta’adda a garin Ruwan Godiya da ke ƙaramar hukumar Faskari.
Rundunar sojojin da aka fi sani da ‘FARAUTAR MUJIYA’, sun kai hare-hare ne a maɓoyar ƴan ta’adda a garin inda suka lalata sansanin ƴan ta’addan da kashe wasu da dama daga cikin su.
Kwamishinan Cikin gida da Tsaro, Dakta Nasiru Mu’azu Ɗan-Musa ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a inda ya ce ƙoƙarin da jarumta da sojojin suka nuna za su ƙara kwantar wa al’umma da hankali.
“Ƙwarewa da ƙwazo da sojojin suka nuna wajen ƴanto garin Ruwan Godiya babu shakka ya nuna ƙoƙarin da suke yi na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar, musamman wuraren da ƴan ta’addan suke addaba”, inji Ɗan-Musa.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bai wa gwamnati goyon baya wajen ƙoƙarin da ta ke yi na kakkaɓe ƴan ta’adda a jihar.
