Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da makarantun sakandire 75 da AGILE ta gina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban Tsarin Ilimin bai ɗaya na jihar Dakta Kabir Magaji, ya bayyana shirin na AGILE a matsayin shiri da ke bada gagarumar gudunmuwa wajen cigaban ilimi a Jihar Katsina.

Ya ce cikin makarantun sakandiren guda 75, 45 daga cikin su ƙananan sakandire ne (junior section), sauran kuma manyan sakandire (Senior).

A nata jawabin, Kwamishinar Ilimi ta jihar, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana ƙaddamar da buɗe makarantun a matsayin wani abin tarihi a fannin ilimi a Katsina, ta na mai cewa shirin na AGILE ba ƙaramin cigaba ya kawo a jihar ba.

Kodinetan shirin AGILE ta Ƙasa, Misis Amina, ta nuna gamsuwa da irin ingantaccen gini kuma na zamani da aka yi wa makarantun inda ta ce an yi shi daidai da zamani wanda ɗalibai za su gudanar da karatukansu cikin yanayi mai daɗi.

Haka ma, kodinetan AGILE na jihar, Dakta Mustapha Shehu ya faɗi duk nasarorin da shirin ya samu a Katsina, ya na mai nasabta su da irin goyon baya da Gwamna Dikko Raɗɗa ke ba su wajen gudanar da ayyukansu.

Ya a ƴan kwanakin nan ne aka samu wasu makarantun da gwamnan ya amince masu da fara aiki.

Ya ƙara da cewa, a shekarar 2019, jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da ɗalibai ba sa cigaba da karatu bayan gama firamare ko ƙaramar sakandire, amma a yanzu rashin cigaba da karatu ya ragu a jihar Katsina da kaso 40.

Daraktan bankin duniya a Najeriya, Dakta Ndiame Diop, ya yi godiya ga Raɗɗa bisa karramawar da aka yi masa inda ya ce, “na daɗe ina jin ana faɗin Katsina gidan kara yanzu kuma na tabbatar da hakan da kai na.”

Ya kuma yaba da aikin da aka yi wa makarantun da zai bai wa ɗalibai damar gudanar da karatukansu cikin nitsuwa da kwanciyar hankali, sannan kuma ga kuɗi da ake tallafawa musu da su wanda zai ƙara masu ƙwarin-gwiwar yin karatu kuma zai rage yawan yaran da basa zuwa makaranta.

A jawabin ƙaddamar da Makarantun, Gwamna Raɗɗa ya yi godiya ga shirin na AGILE game da irin gudummuwar da ya ke badawa a jihar.

Ya kuma ce, cigaban ilimi na ɗaya daga cikin ƙudirorin gwamnatinsu.

“shi yasa muka ɗauki malaman makaranta 7,325 ba tare da nuna sanayya ko ɓangarenci ba”, inji shi.

By Babaji