Maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi ya rasu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Tsohon sakataren hukumar zaɓe na kasa maraɗin Katsina kuma Hakimin kurfi ya rasu.

Ya rasu a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina yana da shekara 90.

Marigayi Ahmadu kurfi ya taba riƙe sakataren hukumar zaɓe na ƙasa(FEDECO) a shekarar 1999.

Kafin nan marigayin ya fara aiki a mulkin Sardauna Ahmadu Bello a 1958 .

Ya kuma riƙe muƙamin babban sakatare a ma’aikatun gwamnatin tarayya guda uku kafin ya ajiye aiki a shekarar 1986.

Daga nan ne ya sami sarauta maraɗin Katsina Hakimin kurfi.

By ukarofi