DAGA JOHN DOGO WADA, a Keffi
A yayin da al’ummar Musulmi a duniya baki ɗaya ke cigaba da bukukuwan bikin ƙaramar sallah, shugaban ƙaramar hukumar Kokona a jihar Nasarawa Hon. Agbawu Mek Agbawu yayi kira na musamman ga al’ummar Musulmi da ma Kiristoci baki ɗaya dake ƙaramar hukumar Kokona da jihar dama ƙasa baki ɗaya su tabbatar suna yin aiki da duka darusa da kyawawan halayya da suka koya a lokacin azumin Ramadan da na Kiristoci da aka gudanar a lokaci guda a bana.
Hon. Agbawu Mek Agbawu yayi kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ciki har da wakilin mu a ofishin sa dake sakatariyar ƙaramar hukumar ta Kokona a garin Garaku ranar Sallah.
Yace kiran ya zama wajibi idan akayi la’akari da mahimmancin ibada da son juna da kuma uwa uba zaman lafiya da sauran su cikin al’umma.
Yace ya tabbata idan duka al’ummomi biyun wato Musulmi da Kiristoci za su danne zuciya kowa yayi aiki da duka darusan azumin, tabbas za a samu canje-canje da dama da kuma albarkatun Ubangiji a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ƙaramar hukumar Kokona Hon. Agbawu Mek Agbawu ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana cewa kaɗan daga cikin ɗimbin ayyukan cigaba da nasarori da gwamnatinsa ta cimma zuwa yanzu da hawan sa kujerar shugaban ƙaramar hukumar sun haɗa da inganta harkokin ilimin zamani da na addini a yankin da gyaran motocin ƙaramar hukumar da suka lalace aka kuma yi watsi dasu da daɗewa da inganta harkokin noma inda har ta kai ƙaramar hukumar tayi gonar kanta kuma an samu alheri daga girbin da aikin gina sabon gidan shugaban ƙaramar hukumar ta Kokona da gina sabbin bohole-bohole a duka gundumomin ƙaramar hukumar guda 11 da aikin gina sabbin hanyoyin cikin gari a nan Garaku da kewayen ta da kuma uwa uba tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar sa inda gwamnatinsa ke haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule don cimma burin tsaro da sauran su.
Dangane da ƙalubalai da ƙaramar hukumar ke fuskanta sai Hon. Mek Agbawu ya bayyana cewa a da sun yi ta fuskantar batun rashin zaman lafiya ne a yankin a matsayin babbar ƙalubalai amma a yanzu hakan yazama tarihi sakamakon aiki tuƙuru da gwamnatinsa ke yi da haɗin kan gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ba dare ba rana don magance lamarin.
A ƙarshe sai shugaban ƙaramar hukumar ta Kokona Hon. Agbawu Mek Agbawu ya kuma yi amfani da damar inda ya taya duka al’ummar Musulmi da ke yankin sa da jihar baki ɗaya murnar bikin ƙaramar Sallar bana inda yayi fatar Allah ya kai kowa na baɗi ya kuma amshi duka addu’oin su da ibadun su da sauran su da suka ɗauki lokuta suna yi a yayin azumin.
Shi dai shugaban ƙaramar hukumar ta Kokonan na yanzu wato Hon. Agbawu Mek Agbawu ƙarin binciken wakilin mu ya gano cewa tabbas ana cigaba da samun dawamammiyar zaman lafiya a yanzu haka a ƙaramar hukumar da kewayen ta baki ɗaya ƙarƙashin jagorancin sa saɓanin yadda lamarin yake a da, kuma al’ummar ƙaramar hukumar da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule kan sa na cigaba da yaba masa a wannan ƙoƙari da yake yi na tabbatar da tsaron yankin.
