An gudanar da taron addu’o’in neman zaman lafiya a Kano

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani babban ɗan kasuwar gwari a Legas, Alhaji Ubale Babu Munafinci, dan asalin Karamar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ya jagoranci wani gagarumin taron addu’o’in neman karin zaman lafiya a Kano, Legas da ma kasa baki daya.

Taron wanda aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, ya gudana ne a harabar kofar gidansa da ke garin Kiru, inda ya samu halartar manyan malamai, shugabannin al’umma, ’yan kasuwa daga kasuwar Mile 12 International Market da ke Legas, da kuma dimbin jama’a daga sassa daban-daban na Karamar Hukumar Kiru da kewayenta.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Injiniya Kabiru Kiru, da wasu daga cikin shugabannin ’yan kasuwar Mile 12, ciki har da Alhaji Dauda, tsohon sakataren bangaren kasuwanci na kasuwar, da kuma Alhaji Kabiru Yalo da sauransu.

Haka kuma, uban taron, Alhaji Yusuf Isma’il, mai garin Cunkoso da ke Karamar Hukumar Madobi, ya halarci taron tare da sauran manyan baki.

A yayin buɗe taron, malamai sun gabatar da wa’azuzzuka ga al’ummar Musulmi dangane da muhimmancin watan azumin Ramadan, inda suka jaddada bukatar taimakon juna, ciyar da mabuƙata da kuma tsare ibadu a wannan lokaci mai alfarma.

Malaman sun kuma karanta ayoyin Alkur’ani mai tsarki tare da gudanar da addu’o’i na musamman, suna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano, Legas da ma Nijeriya baki daya.

A wani ɓangare na taron, Babban Limamin Masallacin Juma’a na garin Kadauji, Malam Sha’aibu Kadauji, ya jagoranci daurin aure na wasu daga cikin ‘ya’yan Alhaji Ubale, inda aka daura auren Ziladaini da amaryarsa Malama Humaira, da kuma Isma’il da amaryarsa Malama Lauratu.

An gudanar da ɗaurin auren cikin walwala tare da addu’ar Allah Ya ba ma’auratan zaman lafiya, kauna da albarka a rayuwarsu.

Da yake jawabi a karshen taron, Alhaji Ubale Babu Munafinci ya nuna matukar godiya ga dukkan wadanda suka halarci taron, musamman tawagar ’yan kasuwar Mile 12 karkashin jagorancin shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam.

Ya yaba da haɗin kai da goyon bayan da shugabannin kasuwar ke bayarwa wajen bunkasa harkokin kasuwanci, tare da kira ga sauran ’yan kasuwa da su ci gaba da mara musu baya domin cigaban kasuwar gaba daya.

Hakazalika, ya yi fatan alheri ga mahalarta taron, yana rokon Allah Ya mayar da kowa gida lafiya tare da karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma.

By ukarofi