Ƙaranci da tsadar fetur: Mataimakin Shugaban ƙasa ya gana da Lokpobiri, Kyari da Ribadu don neman mafita

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya gayyaci ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri; da Babban Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin Mai na NNPC, Mele Kyari.

Blueprint Manhaja ta kuma ruwaito cewa, an gayyaci Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, a jiya Alhamis a Fadar Shugaban ƙasa kan ƙarin farashin man fetur da kuma ƙarancinsa a Nijeriya.

Shettima ya gana da mutanen ukun ne a ofishinsa na fadar Gwamnatin Tarayya Abuja.

A ranar Talata ne kamfanin NNPC ya kara farashin man fetur daga N568 zuwa N855, N897 (ya danganta).

Wasu gidajen mai masu zaman kansu sun riga sun sayar da man fetur a farashi mafi yawa fiye da NNPCL. Wasu dai na sayar da shi kan Naira 1,200 kan kowace lita a ranar Laraba.

Ƙarin farashin dai ya zo ne kwana guda bayan da kamfanin mai na ƙasa NNPC ya amince cewa yana fama da matsalar rashin kuɗi.

A ranar Laraba a Legas da Abuja da kuma birnin Kano da ke Arewacin ƙasar, an rufe wasu gidajen mai masu zaman kansu yayin da manyan layukan motoci ke dakon dare a wajen gidajen man NNPC.

‘Yan Nijeriya da ƙungiyoyi da dama sun yi Allah-wadai da hauhawar farashin man fetur na NNPC a cikin wahalhalu da yanayin tattalin arzikin da ‘yan ƙasar ke fuskanta.

Daga cikinsu akwai ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya NLC, Trade Union Congress (TUC), ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya NBA da ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NMA), suna masu cewa ƙarin zai ƙara wa ‘yan Nijeriya wahalhalu..

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya yi Allah wadai da ƙarin farashin man fetur, ya kuma zargi gwamnati da cin amanar ƙungiyar ƙwadago. Ya buƙaci a sauya farashin man fetur nan take.

“Muna buƙatar a gaggauta sauya sabon ƙarin da aka samu na fetura faɗin ƙasar, a saki duk waɗanda ake tsare da su ko kuma ana tuhumar su bisa zaton sun shiga zanga-zangar kwanan nan,” in ji Ajaero.

Ƙungiyar Likitocin Nijeriya reshen jihar Legas, ta buƙaci Shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya sake duba manufofin gwamnatinsa na tattalin arziki tare da rage farashin man fetur.

Shugaban NMA na Legas, Dakta Saheed Kehinde, ya yi Allah-wadai da ƙarin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan, inda ya bayyana cewa ya ɗora wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da ba za su iya jurewa ba, da suka haɗa da ƙwararrun likitoci, waɗanda tuni ke fama da matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.

A cewar Kehinde, yawancin mambobinsu na barin ƙasar ne saboda taɓarɓarewar tattalin arziki, kuma wannan ci gaban da aka samu a baya-bayan nan zai ƙara dagula halin da suke ciki.

To, amma jim kaɗan bayan kammala ganawar Mataimakin Shugaban ƙasa da masu ruwa da tsakin da ya kira a Fadar Shugaban ƙasa jiya, ƙaramin Ministan Mai, Mista Heineken Lokpobiri, ya shiada wa manema labari cewa, kada a razana da yanyain da ake ciki a ƙasar, domin gwamnati ta shirya magance ƙalubalen.

“Shugaban ƙasa, wanda ba ya ƙara a halin yanzu ne ya umarci Mataimakin Shugaban ƙasa da ya shirya ganawar, kuma mun yi masa bayanin halin da ake ciki.

“Mu na shaida wa ’yan Nijeriya cewa, Shugaban ƙasa ya na tausayin halin da suke ciki a ƙasar. Ya na damuwa da halin ƙuncin rayuwar da ’yan Nijeriya ke ciki. Don haka nema ya bayar da umarnin a yi zaman, don duba yanayin abubuwan da ke faruwa a cikin ƙasar.

“Akwai isasshen fetur a ƙasar, kuma mun yi imanin cewa, daga yanzu zuwa ƙarshen mako za a samu isasshen fetur a faɗin ƙasar. Za a iya samun tsadar farashin a wasu guraren fiye da wasu, amma mun yi imanin cewa, duk lokacin da kaya ya wadata, shi kansa farashin yana daidaita,” inji shi.

Matatar Mai ta ɗangote ta bayyana cewa Kamfanin Mai na ƙasa (NNPC) bai fara sayen fetur daga gareta ba.

Sanarwar da Matatar ɗangote ta fitar ta ce kamfanin bai ma kammala ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da NNPC kan tataccen man fetur ɗinsa ba, ballantana NNPC ya fara ɗaukar man domin sayarwa.

Kamfanin ya ce ya yi wannan bayani ne sakamakon wasu labarai marasa tushe da ke cewa NNPC ya fara ɗaukar man fetur daga Matatar ɗangoye domin sayar da lita a kan N897.

Amma hukumar gudanarwar Matatar ɗangote ta ce “ba mu kammala yarjejeniyar sayar da tataccen man ga NNPC ba, ballantana maganar farashi ta taso.”

Wannan bayanin yana ƙunshe ne a cikin sanarwar da kakakin Matatar ɗangote, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

A ranar Talata ne dai Matatar ɗangote da sanar a hukumance cewa ta fara fitar da tataccen man fetur kuma da zarar sun kummala ƙulla yarjejeniyar da NNPC man zai shiga kasuwa.

Shugaban Rukunkin Kamfanonin ɗangote, kuma mamallakin matatar, Alhaji Aliko ɗangote, ya ce ingancin man fetur ɗin matatar zai yi goyagga da na ƙasar Amurka da manyan ƙasashen duniya, kuma ba shi da illa ga injina.

A cewar ɗangote, aikin matatar zai rage wa Nijeriya dogaro a kan Dalar Amurka da kashi 40 cikin 100.

Hukumar harkokin mai (NMDPRA) ta sanar cewa matatar za ta fara samar da lita miliyan 25 na fetur a kullum a cikin gida a Nijeriya, zuwa watan Oktoba kuma za a ƙara yawansa zuwa lita militan 30.

A safiyar jiya, a shirin safe na AriseNews, Mista Adedapo Segun, mataimakin shugaban NNPC, ya bayyana cewa matatar ɗangote tsakanin watan Satumba zuwa Nuwamba za ta samu ƙarin ganga miliyan 17.8 na ɗanyen mai a wani ɓangare na ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin an samar da man fetur a cikin gida.

Kawo yanzu dai kamfanin NNPC ya samar da gangar ɗanyen mai miliyan 30 ga matatar don fara aiki. Matatar ɗangote ta sanar a farkon makon nan, a wani taron manema labarai da shugaban kamfanin Aliko ɗangote, ya yi jawabi, cewa yanzu a shirye suke su saki mansu a kasuwa.

A cewar Mista Adedapo Ganga miliyan 6.8 a cikin 7 na ɗanyen mai za a kai matatar ɗangote a watan Satumba, yayin da za a kai wasu ganga miliyan 11 a watan Nuwamba.

Ya ci gaba da bayyana dalilin da ya sa kamfanin na NNPC ya kasance mai shigo da fetur a ƙasar nan, inda ya ce yanayin kasuwa bai sa ‘yan kasuwa masu zaman kansu su iya shigo da fetur ba sakamakon rashin sahihanci da farashin famfo da ya yi ƙasa da kuɗin saukewa.

Saɓanin rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa cewa matatar ɗangote za ta sayar wa kamfanin na NNPC ne kawai a matsayin mai ɗauka, Mista Adedapo ya ce ɗangote zai sayar da mansa ga sauran ‘yan kasuwa da zarar yanayin kasuwa ya dace, inda ya ce a yanzu kamfanin na NNPC zai yi aiki a bainar jama’a a matsayin mai ba da mafita ta ƙarshe kamar yadda aka tanadar a cikin Dokar Masana’antar Man Fetur.

Shugaban ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (PETROAN), Billy Gilly-Harry ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su shirya tsaf domin fuskantar ƙarin farashin man fetur) nan da kwanaki masu zuwa, yana mai cewa daga yanzu za a siyar akan farashin kasuwa.

Gilly-Harry ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake magana a matsayin baƙo a wani shiri da Channel ke gabatarwa.

Da aka tambaye shi ko ya kamata ‘yan Nijeriya su yi shirin ƙarin farashin, sai ya ce “A gare ni, abin da zan ce shi ne in ƙarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya su sayi man fetur a farashin da ‘yan kasuwa suka ƙayyade. Duk da haka, muna da cikakkiyar masaniyar cewa tallafin man fetur na nau’ikan kayayyaki daban-daban a faɗin duniya, da mai da iskar gas albarkatu ne ga ‘yan Nijeriya.

Ƙungiyar marasa rinjaye a majalisar wakilai ta yi kira da a gaggauta sauya farashin man fetur da aka yi a baya bayan nan, inda ta ce ko shakka babu hakan zai ƙara wa ‘yan Nijeriya wahala.

ƙungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce matakin bai ɗaya na ƙara farashin fetur, ta yi watsi da ƙa’idojin nuna gaskiya, da riƙon amana, da adalci, waɗanda ya kamata su jagoranci yanke shawara da suka shafi rayuwar ‘yan ƙasa.

Sanarwar da shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda ya yi mai taken “sake farashin man fetur yanzu” ya buƙaci shugaban ƙasar da ya gaggauta samar da matakan gaggawa don magance alaƙar da ke tsakanin mummunan yanayin tattalin arziki da tashe-tashen hankula a cikin al’umma maimakon haifar da yanayin da ke ƙara ta’azzara yanayin tattalin arzikin da ake ciki.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A daidai lokacin da al’ummar ƙasar ke fama da ƙalubalen tattalin arziki da ba a taɓa ganin irinsa ba, da suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi, da faɗuwar darajar Naira, duk wani ƙarin farashin man fetur zai ƙara ta’azzara wa talakawan Nijeriya wahala.

“Sakamakon irin wannan ƙaruwar yana da yawa, yana tasirantuwa a farashin sufuri, abinci, da sauran kayayyaki da ayyuka masu muhimmanci. Wannnan zai tura ƙarin iyalai cikin talauci.

“Ƙungiyar Marasa Rinjaye ta damu matuƙa da cewa ga dukkan alamu an yanke wannan hukunci ne ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki ba ciki har da Majalisar Dokoki ta ƙasa wadda ke wakiltar muradun al’umma. Wannan mataki na bai-ɗaya ya yi watsi da ƙa’idojin bayyana gaskiya, da riƙon amana, da adalci, waɗanda ya kamata su jagoranci yanke shawara da suka shafi rayuwar ‘yan ƙasa. Mummunan yanayin tattalin arziki da ake fama da shi a halin yanzu, wanda ke tattare da ƙaruwar rashin aikin yi, hauhawar farashin kayayyaki, da sauransu.

“Waɗannan wahalhalun sune suka haifar da zanga-zanga, yayin da mutane ke neman agaji da kuma ɗaukar nauyin masu riƙe da madafun iko. Sakamakon tashe-tashen hankula da hargitsi sun zama abin tunatarwa cewa rashin kwanciyar hankali na tattalin arziki na iya rikiɗewa cikin sauri zuwa mafi girman rashin zaman lafiya. s

“Dole ne wannan gwamnati ta koyi darasi daga illolin da zanga-zangar adawa da rashin shugabanci na gari ke haifarwa, wanda ya jawo taɓarɓarewar yanayin tattalin arziki.

“Saboda haka, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggawar shiga tsakani, ta kuma kawo ƙarshen wannan ƙarin farashin man fetur da ba a yarda da shi ba. Muna kuma roƙon gwamnati da ta binciko tare da aiwatar da wasu matakai masu ɗorewa don daidaita tattalin arzikin ƙasar ba tare da ɗora wa jama’a wani nauyi ba.”

By ukarofi