
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ce ta yi kwaskwarima ga kuɗin alawus da ta ke bai wa dukkan ƴan fursunan da ke gidajen yarin Nijeriya inda ta ƙara musu kaso 50 kan yadda ta saba biya.
Rahotonni sun bayyana cewa, matakin ya biyo bayan wata ɗaukar bidiyo ne da ta karaɗe kafafen sadarwa inda aka ga wasu ƴan fursuna su na ƙorafi kan irin ƙasƙantaccen ciyarwa da ake musu a gidan kurkukun Calabar da ke jihar Cross-River.
Mai magana da yawun Hukumar da ke Kula da Gidajen Yari (NCoS), Umar Abubakar ya faɗi hakan a hedikwatar hukumar da ke Abuja a wani taron ganawa da manema labarai da hukumomin tsaro suka yi.
Ya ce, ƙarin shi ne ɓangare na farko na ƙoƙarin magance matsalolin tsadar abinci a Nijeriya, ya na mai cewa abin da bidiyon ya nuna ba shi ne haƙiƙanin yadda NCoS ta ke yi ba a yayin kula da fursunoni.
Ya ƙara da cewa, hukumar na iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta bai wa ƴan fursuna horarwar da ta dace ta yadda za su koma cikin al’umma su na masu nagarta da kuma dogaro da kansu saboda koyon haka a yayin zamansu na gidajen yari.
