Man fetur zai wadata nan da ƙarshen mako – Ministan mai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Albarkatun Man fetur, Heineken Lokpobiri ya ce za a samu isasshen man fetur nan da ƙarshen wannan satin.

Ya faɗi hakan ne a yayin wani zama da Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari da kuma shugaban Hukumar tace Ɗanyen Man fetur, Mugo Okuoha a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya ce, al’umma su kauce wa sayen man fetur a farashin da ya wuce kima, ya na mai bada albishir da cewa farashin zai yi sauƙi yayin da aka samu yalwataccen mai acikin al’umma.

Ya ƙara da cewa, shugaba Tinubu ya damu da halin matsin da al’umma ke ciki, don haka akwai buƙatar samuwar isasshen mai ga mutanen ƙasa duk da cewa farashin ka iya banbanta la’akari da wurare.

Yayin da ƙarin man fetur ɗin ya sanya NNPCL ke sayer da lita a tsakanin N855 da N897, gidajen mai na ƴan kasuwa kan sayer a N930 zuwa N1,200.

Hakan wani lamari ne da ya sabbaba wasu ke tattaki zuwa wajen harkokinsu yayin da wasu kan rasa zuwa wajen ayyukansu saboda tsadar kuɗin sufuri.

By Babaji