Obasanjo, Osinbajo da Zullum sun je ta’aziya ga iyalan Dada Musa Yar’adua a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo da kuma gwamnan Jihar Borno sun zo katsina ta’aziyar Marigayiya Dada Musa Yar’adua.

Da yake jawabi da iyalan marigayiyar, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya bayyana rasuwar Hajiya Dada Musa Yar’adua a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya .

Yace shi a wajan marigayiyar uwa ce gare shi ganin yadda ya ke da kusanci ga ya’yan ta da tun yana da ƙurucciya su ke tare .

Ya ƙara da cewa wani abinda ba zai taɓa mantawa da shi ba shine yadda marigayiya Dada Musa Yar’adua ta tashi daga Katsina har zuwa Abeokuta domin tayi godiya da ɗanta wanda nima ɗan’uwa na ne marigayi Umaru Musa Yar’adua da ya zama shugaban ƙasa.

Ya kuma godewa gwamna Dikko Raɗɗa da a ko da yaushe ya ke masa bayanin halin da ta ke ciki.

Tsohon shugaban ƙasar ya nuna cewa kulawa da ta ke samu daga ƴaƴanta a lokacin da ta ke raye ya sa ta daɗe cikin koshin lafiya har ta yi kyakkyawar ƙarko .

Shima tsohon mataimakin shugaban ƙasa yemi Osinbajo yakai nasa ziyarar ta’aziya gidan marigayiyar ya bayyana Hajiya Dada Musa Yar’adua mutumiyar da ta bautawa ƙasa ta hannun manyan ya’yan ta

“Hajiya Dada Musa Yar’adua bawai yar jihar Katsina bane kawai,yar Nigeria ce da shiyasa mutane daga ko ina cikin ƙasarnan suke ta tururuwa zuwa ta’aziya ga iyalanta”Osinbajo yace.

“Wasu a cikin mu da mu ka san ta a lokacin rayuwar ta, mace ce mai kamala da natsuwa da rashin magana da kuma kyautatawa al’ummar ta” ya faɗi haka

“Mijinta yayi minista ɗanta yayi shugaban ƙasa ɗaya kuma yayi mataimakin shugaban ƙasa ga wani kuma yanzu yana sanata”.

Osinbajo ya cigaba da cewa Hajiya Dada mace da ta yi aiki tuƙuru ta ga ta baiwa mijin ta da ya’yan ta ƙarfin gwiwa su bautawa ƙasa wanda Allah ya kai su inda suka kai har zuwa lokacin da wasu su ka koma ga mahaliccin su .

Tunda farko sai da gwamna Dikko Raɗɗa ya raka gwamnan Jihar Borno, Babagana zullum,zuwa
gidan Yar’adua inda ya yi wa iyalan marigayiyar addu’ar Allah yafe mata kurakuranta.

Shima ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar Labor Party Peter Obi wanda da shi akayi jana’izar ya bayyana ta a matsayin mace da ta ga jiya ta ga yau .

Cikin waɗanda suka zo ta’aziyar akwai tsohon gwamnonin Gombe da Kebbi Sanata Danjuma Goje da sanata Adamu Alheri da kuma sanata Abdul Ingila

By ukarofi