Ƙarancin fetur da gabatowar zaɓe

Duk da alqawarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe a wannan shekara, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta yi gargaɗin cewa matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da shi na iya kawo cikas ga zirga-zirgar kayayyaki da ma’aikata a ranakun zaɓe, idan ba a gaggauta magance shi ba.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana fargabar da ke tattare da zaɓen 2023 a wani taron tuntuvar juna da Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Jiragen Ruwa ta Ƙasa (NURTW) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ruwa ta Nijeriya (MWUN) kan zaɓen da ke tafe.

Shugaban na INEC ya kuma gana da Babban Manajan Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL), Mele Koko Kyari, kan batun. Ko da yake Kyari ya ba shi tabbacin samar da isassun mai a lokacin zaɓe, ƙarancin man na ci gaba da yin illa ga sauran ɓangarorin tattalin arziki. ’Yan Nijeriya dai na cikin yanayin ƙunci sakamakon ƙarancin man fetur da kuma canjin sabbin takardun kuɗi na Naira.

Duk waɗannan za su shafi motsin kayan aiki da ma’aikata yayin zaɓe. Ana sa ran za a kai kayan zaɓen zuwa rumfunan zaɓe kafin a fara atisayen. Hakazalika jami’an INEC da ma’aikatan wucin gadi su kasance a rumfunan zaɓe kafin zuwan masu kaɗa ƙuri’a.

Ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin an samar da isasshen man fetur kafin zaɓe da lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe. Ƙarancin man fetur ya janyo tashin farashin sufuri da tsadar rayuwa. Idan har ta ci gaba, zai yi tasiri sosai kan harkokin gudanar da zaɓe.

Babu shakka, man fetur shine jigon motsi da samar da walwala a Nijeriya. Duk wani abu da zai kawo cikas ga wadatarsa ya kan yi illa ga ƙasa. Abin baƙin ciki ne yadda ’yan Nijeriya ke fama da wahalhalu da ba za a iya kauce musu ba a lokacin zaɓe. Don haka dole ne gwamnati ta gaggauta magance matsalar makamashi tun da wuri kafin zaɓe. Idan har ya daɗe, to ko shakka babu zai yi tasiri wajen gudanar da zaɓen.

Ba ga shugaban ƙasa kawai ba, ya kamata INEC da sauran hukumomin da abin ya shafa da aka ɗorawa alhakin zaɓen su ba da tabbacin cewa dole ne a gudanar da zaɓen yadfa yakamata. Dole ne gwamnati ta gaggauta magance duk wasu al’amura da za su kawo cikas ga gudanar da zaɓen. Zaben 2023 na da matuƙar muhimmanci ga ɗorewar dimokaraɗiyyarmu da ƙasa. Haƙiƙa, zaɓe ɗaya daga cikin abubuwan masu ma’ana sosai ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya. Don haka, duk wani abu da zai cutar da zaɓen, ya kamata a magance shi nan da nan.

Kwamitin gudanarwa mai mambobi 14 da gwamnati ta kafa kwanan nan ya kamata ya fito da shawarwarin yadda za a magance matsalar. Muna kira ga kamfanin NNPC da masu sayar da man fetur da su yi aiki tare da tabbatar da cewa an samu isasshen man fetur.

’Yan Nijeriya sun gaji da ƙarancin man fetur da kuma layukan da ake fama da su a gidajen mai. Akwai buƙatar kawo ƙarshen irin waɗannan matsaloli na shekara-shekara sakamakon ƙarancin man fetur. ’Yan Nijeriya sun cancanci samun fetur a araha kuma ba tare da katsewa ba.

Har ila yau, rashin tsaro, tashe-tashen hankula, taɓarɓarewar kuci da sayen ƙuri’u, wasu ƙalubale ne da ya kamata a yi taka-tsantsan akansu domin ‘yan Nijeriya su yi zaɓe mai inganci. Duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da tsaro, ana ci gaba da kai hare-hare kan jami’an hukumar ta INEC da wasu wurare.

A ranar 1 ga watan Fabrairu ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari ofishin INEC da ke Ojoto a Ƙaramar Hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra. ’Yan ta’addan sun kuma kai hari ofishin ’yan sanda na Nnobi da wani gini da ke cikin ofishin, wanda shi ma a Unguwar Kansila. An kashe wani yaro ɗan shekara 16 yayin da wata yarinya ’yar shekara 15 ta samu mummunar rauni a yayin harin.

Harin da aka kai a cibiyar INEC a Anambra ya zo ne makonni kaɗan bayan wani hari makamancin haka a jihar Enugu inda aka kashe wani xan sanda. A wani wuri kuma, lamarin bai bambanta ba. A cikin shekaru huɗu da suka gabata, hukumar ta fuskanci hare-hare sama da 50 a cibiyoyinta a faɗin ƙasar.

Haka kuma, kalami marasa daɗi da ‘yan siyasa da magoya bayansu ke yi na iya kawo cikas ga zaɓen. A sa a masu isassun kuɗaɗe a ƙasar domin kada masu kaɗa ƙuri’a su faɗa cikin jarrabawar sayar da ƙuri’unsu ga ’yan siyasa marasa kishin ƙasa.

Ya zama wajibi gwamnati ta samar da yanayi mai kyau ga masu kaɗa ƙuri’a don yin amfani da ikonsu da zaɓar shugabanni masu nagarta. Kada a bar matsalar man fetur ta tauye musu haƙƙinsu na zaɓen shugabanni na gari. Gwamnati na da isasshen lokacin da za ta tunkari ƙalubalen da ke gaban zaɓen ta yadda INEC za ta iya gudanar da zaɓe mai inganci.