A bari a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira – Majalisa

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Tarayya ta ce akwai buƙatar Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bari a ci gaba da amfani da tsofaffi da sabobbin takardun Naira tare.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu a ranar Juma’a.

Ya ce yin hakan zai taimaka wajen sauƙaƙe wa ‘yan ƙasa wahalar ƙarancin kuɗi da ake fuskanta a halin yanzu.

“Mu a Majalisar Dattawa, da farko mun ɗauka babu wata matsala tattare da tsarin, kuma muna jin ce babu buƙatar ƙayyade wani wa’adi, a bari a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira da sabbin tare a hankali har tsofaffin su ɓace,” in ji Lawan.

Ya ƙara da cewa, lamarin ba zai cim ma nasara ba a ce komai ya daidaita cikin wata uku, “musamman kuma a ƙasa irin tamu.”

Ya ce ba Nijeriya ce ƙasa ta farko da ta fara yin hakan ba, wasu ƙasashen sun gwada.

Yanzu ne lokacin da ya kamata a ɗauki mataki kan batun ta hanyar sake kallonsa kan yadda ya kamata a siwatar da shi.

“Kowa ya san yadda galibin ‘yan Nijeriya ke fama da wahala a sassan ƙasa, musamman kuma talakawa, hakan ya sa muka ji cewa yanzu ne ya dace a ɗauki matakin da zai sassauta wa ‘yan Nijeriya matsin da suke fuskanta,” in ji Lawan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *