Dalilin fuskantar ƙarancin sabbin takardun Naira – Emefiele

Daga WAKILINMU

Babban Bakin Nijeriya ta bakin shugabansa, Godwin Emefiele, ya bayyana dalilin da ya haifar musu da tsaiko wajen samar da sabbin takardun Naira da aka sauya wa fasali a wadace.

A Emefiele, a halin yanzu Babban Bankin ba shi da halin buga sabbin takardun kudin da za su wadata kasar saboda takardun da ake buga kudin da su sun yanke.

Ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin da yake yi wa Majalisar Ƙasa jawabi kan batun sauya fasalin takardun Naira.

Majiyar Jaridar Premium Times da ta halarci zaman Majalisar ta ruwaito cewa, Emefiele ya koka kan yadda yankewar takardun da ake amfani da su wajen buga kuɗi ta haifar da cikas.

Emefiele ya shaida wa Majalisar cewa Kamfanin Buga Tsabar Kudi na Ƙasa wato Nigerian Security Printing and Minting Plc, ya gamu da wannan tasgaro na rashin takardun buga kuɗi, dalilin ke nan da ya hana a samu wadatar sabbin takardun N200, da N500 da kuma N1000 da aka sauyawa fasali.

“A halin yanzu takardun buga kuɗin sun kare wa Kamfanin balle a buga ’yan Naira 500 da Naira 1000 da za su wadata ƙasar.

“Sun bayar da odar kawo musu takardun daga wani kamfani a Jamus da kuma wani kamfani mai suna De La Rue da ke Birtaniya, amma har yanzu zaman jiran tsammani ake yi.

Ya ƙara da cewa, “mun miƙa wa Kamfanin buƙatar buga sabbin takardun kuɗi miliyan 70, wanda hakan zai sa a samu ƙarin Naira biliyan 126 zuwa yau (Juma’a) suna yawo a tsakanin al’umma, amma hakan bai samu ba saboda yankewar takardun.