Sanata Bwacha ya zama ɗan takarar Gwamna na APC a Taraba

Daga WAKILINMU

Sanata Emmanuel Bwacha ya lashe zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar (APC) da aka maimaita a matsayin ɗan takarar gwamna na Jihar Taraba .

Wannan na zuwa ne yayin da zaɓen gwamnoni ya ƙarato, wanda za a gudanar 11 ga Maris.

A zaɓen da aka sake, Bwacha ya samu ƙuri’u 778 yayin da abokin hamayyarsa, Yusuf Yusuf ya damu biyar.

Baki ɗaya, dalaget 796 aka tantance yayin zaɓen.