Mutane 25,000 suka ɓace sakamakon rikici a Arewa maso Gabas Nijeriya – ICRC

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahotannin dai sun bayyana cewa, aƙalla mutane 25,000 ne suka yi bayan dabo a sakamakon rikice-rikicen da aka sha fama da su a Arewa maso gabashin Nijeriya. 

Wannan rahoto ya fito daga masu ruwa da tsaki a kan masu taimaka wa iyalan waɗanda suka vace ɗin. A yayin wani taro da suka gabatar ranar Litinin ɗin da ta gabata don tabbatar da cewa ba a mance da iyalan waɗanda suka ɓace ɗin ba wajen tallafin da ake bayarwa a ƙasar nan.  

Wannan jawabi dai kwamitin ƙungiyar Red Cross ta ƙasa (ICRC) shi ya wallafa shi, wanda Aliyu Dawobe Pat Griffiths suka sanya wa hannu. An wallafa shi ne don taron masu ruwa da tsaki wanda aka gabatar da haɗin gwiwar Ma’aikatar gwamnatin Tarayya ta jin-ƙai da kula da annoba, da kuma Hukumar kare haqqin mutane ta ƙasa. 

Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa, babban maƙasudin taron ganawar shi ne, don samo bakin zaren game da matsalolin iyalan mutanen da suka ɓace. 

A cewar mataimakin shugaban tsare-tsare na ICRC, Kouame Adjoumani, kowanne mutum da ya vata, ya bar iyalai da dangin waɗanda suke cikin yanayin baƙin ciki da zafin rashin su. 

Adjoumani ya ƙara da cewa, iyalansu sukan shiga yanayi na  matsin tattalin arziki, da wasu matsalolin da za su hana su sake su cigaba da jin daɗin rayuwarsu har ma su sha kan matsalolinsu. 

An shirya taron ne don a haɗa gwiwa don samun hanyoyin da za a warware matsalolinsu, da kuma samar da hanyoyi da tsarin da matakan da za a ɗauka don tallafar dangi da iyalan waɗanda suka ɓata.

Haka zalika, Anne-Sofie Stockman, wakiliya daga iyalan vatattaun ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka bayan za su ma iya haura 25,000 ɗin da aka faɗa.

Kuma a cewar ta, kaso 90 na kesa-kesan vatattaun mutane a Arewa maso gabacin Nijeriya suna da alaƙa da rikice-rikicen sara-suka da suka faru a yankin.