Wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna cewa yawan mutanen da ke fama da matsalar hawan jini a duniya ya ninka biyu a shekara talatin da ta gabata.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kusan mutum biliyan ɗaya da rabi ne ke fama da hawan jini a duniya.
Cikin wani rahoto da hukumar lafiyar ta gabatar kan matsalar hawan jini a babban taron Majalisar ɗinkin Duniya ta ce fiye da mutum 1,000 ne ke mutuwa a kocewa sa’a sakamakon bugun zuciya da mutuwar ɓarin jiki, waɗanda dukkaninsu hawan jini ke haifar da su.
Da yake jawabi, shugaban hukumur WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce akwai buƙatar ƙasashe su tashi tsaye, domin ɗaukar matakan daƙile barazanar hawan jini domin ceto rayukan al’ummar duniya.
”Hawan jini ne babban abin da ke haifar da bugun zuciya da ciwon ƙoda da kuma mutuwar ɓarin jiki – waɗanda ta ce dukkaninsu ana iya magance su”, inji shi
Ya ƙara da cewa, mutum biliyan 1.4 ne ke fama da hawan jini a duniya a shekarar 2024, kuma a cewar rahoton kashi ɗaya ne cikin biyar aka iya magancewa ta hanyar magani da kuma bin matakan da suka dace na lafiya.
Dakta Ghebreyesus ya ce hawan jini na kashe mutum miliyan 10 a kowace shekara, duk da cewa ana iya magance shi.
Hukumar lafiyar ta yi nazari ne a ƙasashe 195, kuma ƙananan ƙasashe ne galibi matsalar ta fi kamari.
”Kashi 28 na ƙananan ƙasashe ne kawai suka bayar da rahoton samun wadatattun maganin hawan jini a ɗakunan shan magani da wuraren sayar da maganin”, a cewar Ghebreyesus .
Ya ci gaba da cewa abubuwan da ke ƙara haifar da matsalar sun haɗa da barasa da taba sigari da kuma rashin motsa jiki da shan gishiri da ya wuce kima a cewar rahoton na WHO.
WHO ta ce idan har hukumomi ba su ɗauki mataki ba, to miliyoyin mutane za su ci gaba da mutuwa ba shiri, wanda zai iya shafar tattalin arzikin ƙasashen duniya.
A ɓangaren Nijeriya kuwa, ƙungiyar Likitocin Zuciya ta Nijeriya (NCS) ta nuna damuwarta yadda cutar hawan jini ke ci gaba da yaɗuwa inda take gargaɗin cewa kashi 40% na mutane na ɗauke da cutar a Nijeriya.
ƙungiyar ta fafi haka ne a taro Karo na 54 da take yi duk shekara domin tattauna hanyoyin inganta lafiyar zuciya.
An gudanar da taron ne tare da taron 17th Biennial Pan African Society of Cardiology (PASCAR) a karkashin taken “Hanyoyin rage farashin cutar cututtukan dake kama zuciya a Afrika”.
Da yake bada jawabinsa a wurin taron tsohon shugaban ƙungiyar NCS Okechukwu Ogah ya ce hawan jini na daga cikin manyan cututtukan dake wa gwamnatin Nijeriya barazana.
“Hawan jini na daga cikin cututtukan dake yi wa mutane kisan farat ɗaya a ƙasar nan.
“Muna da masaniyar cewa kashi 30% na mutane musamman waɗanda suka dara shekara 15 na dauke da cutar wani binciken ya nuna cewa mutum kashi 40% ne ke ɗauke da cutar.
Ogah ya ce, shugabancin da ya yi a ƙungiyar NCS ya yi ƙoƙarin samar da bayanai kan yaɗuwar cututtukan da ke kama zuciya.
Ya ce, ɗaya daga cikin mahimmancin abubuwan da ƙungiyar ta yi shi ne samar da takardar da ke ɗauke da bayanai kan cututtukan da ke kama zuciya da gwamnati za ta iya amfani da shi.
Ya ce, ƙungiyar ta haɗa hannu da Gwamnatin Tarayya domin horar da ma’aikatan jinya kan Kula da masu fama da hawan jini a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko idan babu ƙwararren likita.
Hawan jini na daga cikin rukunin cututtukan da ba a yada su wato ‘Non communicable diseases NCD’ da ake da su a Nijeriya sannan yana daga cikin cututtukan da ke haddasa shanyewar ɓangaren jiki, bugawar zuciya, ciwon ƙoda da kisa.
Bincike ya nuna cewa mutum kashi 30% zuwa 40% a Nijeriya na fama da cutar inda da dama daga cikin su na dauke da cutar ba tare da sun sani ba.
Ƙungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO ta ce cututtukan dake rukunin NCD kamar hawan jini, ciwon siga, ciwon daji, da cututtukan da ke kama nunfashi na daga cikin cututtukan da ke kashe sama da daya da kwatan mutane a Nijeriya.
Masana sun yi gargaɗin cewa Nijeriya na fuskantar annobar cutar hawan jini ta shuru saboda cutar ba ta da wata alama har sai an samu matsala mai tsanani.
Abin takaicin shi ne yadda masu fama da cutar basa samun kulan da ya kamata musamman yadda da dama daga cikin mutanen na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba.
Yawan cin gishiri, rashin motsa jiki, shan taba, shan barasa giya na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar.
ƙarancin asibitoci da tsadar magunguna duk suna cikin matsalolin da masu fama da cutar ke fama da su.
