
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla masu ibada guda biyar ne suka rasu yayin da da dama suka samu raunuka a lokacin da ƴan bindiga suka farmake su a wani masallaci da ke Ƙauyen Ƴandoto a Ƙaramar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara.
Al’amarin ya auku ne a yayin da suke tsaka da gudanar da sallar asubahi, kamar mai sharhi kan al’amuran tsaro Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.
A cewarsa, da misalin ƙarfe 5 na asuba maharan suka kutsa cikin masallacin inda suka ta yin harbe-harbe da buɗe wa masallatan wuta.
Shaidu sun bayyana cewa, a yayin haka ne suka halaka mutane biyar tare da raunata wasu da alburusan bindigunsu.
Wani shaida da ya nemi a sakaye sunansa ya ce maharan sun kuma yi garkuwa da wani adadi na masallatan gabanin su yi koma daji.
Ya kuma ce an garzaya da waɗanda su raunuka zuwa asibiti inda suke karɓar magani kuma suna samun sauƙi a yayin haka.
Hakan na zuwa ne ƙasa daako guda da aka kai irinsa a Ƙauyen Gidan Turbe da ƙaramar hukumar, inda aka yi garkuwa da masallata 40 yayin sallar asuba.
