Daga CMG HAUSA
Rahotannin hukumar kula da kadarorin ƙasa ta majalisar gudanarwar ƙasar Sin sun nuna cewa, karuwar kuɗin shigar manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiyar ƙasar a rabin farko na bana, ta zarce hasashen da aka yi, kuma ingancin ci gabansu yana ƙara kyautatuwa.
Jimillar adadin kuɗin shigar manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta ƙasar Sin, ta kai yuan triliyan 19.2, adadin da ya ƙaru da kaso 12 bisa dari a kan makamancin lokacin a bara.
Kuma jimillar ribarsu, ta kai yuan biliyan 1409.36, adadin da ya karu da kaso 7.1. Kana adadin ribar da suka samu bayan da suka biya haraji, ya kai yuan biliyan 1085.75, adadin da ya ƙaru da kaso 6.1 bisa dari.
An samu wannan ci gaba ne biyo bayan manufofi goma na sa kaimi kan ci gaban manyan kamfanonin ƙasar da hukumar kula da kadarorin ƙasar ta fitar.
Hakazalika, manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta ƙasar Sin, sun ba da babbar gudummowa wajen zuba jari, inda sauran kamfanonin sana’o’i daban daban na ƙasar suka ci gajiya. Ana iya cewa, sun taimakawa bunkasar tattalin arzikin ƙasar Sin matuka cikin watanni shida na farkon bana.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa
