Daga CMG HAUSA
Masaniyar tattalin arziki dake aiki a jami’ar Riala Beatrice ta Kenya, Mathiri-Mysore, ta ce tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya, duk da cewa, kasar tana fama da cutar COVID-19 da sauye-sauyen yanayin siyasar duniya.
Mathiri Mysore, ta bayyana haka ne yayin da take zantawa da manema labaran kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan.
Ta kara da cewa, ƙasar Sin ta gamu da matsala yayin da take fama da yaduwar cutar a wasu sassanta, amma sai ta fitar da manufofi a jere domin daidaita tattalin arzikin cikin nasara.
A ganinta, kuɗin shigar yawancin al’ummun ƙasar Sin yana da yawa, don haka ƙasar ke aiwatar da manufar habaka buƙatun gida, a sa’i daya kuma, ta yi ƙoƙarin kafa sabon tsarin raya ƙasa domin tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arziki.
Mathiri-Mysore ta yi nuni da cewa, har kullum ƙasar Sin tana mai da hankali kan kirkire-kirkire bisa dogaro da kanta, lamarin da ya kai ta ga samun babban ci gaba a fannin sabbin fasahohin zamani.
Har ila yau, ta ce gwamnatin ƙasar Sin ta cimma burinta na tabbatar da lafiyar al’ummunta ta hanyar samar da isassun rigakafin cutar COVID-19 da masanan kimiyya na ƙasar suka nazarta.
A cewarta, abun da ya fi burge al’ummomin ƙasa da ƙasa shi ne, yadda ƙasar Sin ta samar da tallafi ga ƙasashen da suke buƙata a kan lokaci, musamman ma ga ƙasashen Afirka, waɗanda suke fama da yaɗuwar annobar.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa
