Ƙasar Sin ta yi kira da a kyautata dokoki domin samun cigaba mai ɗorewa a ɓangaren teku

Daga CMG HAUSA

Zaunannen wakilin Sin a MƊD Zhang Jun, ya yi kira da a karfafa kiyaye dokoki a ɓangaren harkokin teku domin bunƙasa samun ci gaba mai dorewa.

A cewarsa, tekuna na kyautata rayuwa, kuma suna dauke da albarkatu. Sannan, sun kasance mahaɗar sassan duniya, tare da samar da dandali mai muhimmanci na inganta ci gaba mai ɗorewa. Ya ce a yanzu, tsarin tafiyar da harkokin teku a duniya na fuskantar ƙalubale, kamar gurbatar muhalli da sauyin yanayi, da ƙaruwar matakin teku. Kuma, ƙasa ɗaya tilo ba za ta iya magance wadan nan matsaloli ba, har sai ƙasa da ƙasa sun haɗa hannu wajen ɗaukar mataki.

A cewarsa, ya kamata a haɗa hannu wajen inganta hulɗar ƙasa da ƙasa da kare tsarin hulɗar ƙarƙashin dokokin MƊD, da kiyaye odar ruwan bisa dokokin ƙasa da ƙasa, da yayata aiwatar da ajandar ci gaba mai ɗorewa da ake son cimmawa zuwa 2030.

Haka kuma, ya ce a shirye Sin take ta haɗa hannu da dukkan bangarori wajen kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa da suka shafi harkokin teku da tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kuma ci gaba mai dorewa.

Fassarawar Fa’iza Mustapha