Gwamnatin Kano ta ƙwace gurɓatacciyar fulawa buhu 487

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayen Kaya ta Jihar Kano, KSCPC ta ƙwace kimanin buhun fulawa 487, da ta lalace a wajen ajiyar kaya a kasuwar abinci ta duniya da ke Dawanau da ke birnin Kano.

Manajan-Darakta na riƙo a hukumar, Baffa Babba Ɗan’agundi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin hukumar,  Musbahu Yakasai ya fitar a ranar Talata a Kano. 

Ɗan’agundi ya ce wasu mutanen kirki ne su ka bai wa hukumar bayanan sirri game da fulawar wacce aka kawo kasuwar da nufin sayar da ita. 

Ya ƙara da cewa bayan an kai sumame wajen ajiyar fulawar a kasuwar Dawanau, gwajin da aka yi wa samfurin fulawar ya nuna cewa tuni ta daɗe da lalacewa.

Haka kuma ya ce hukumar ta su ta kama lemuka masu yawan gaske da suka lalace kuma ake sayar da su a kasuwar Sabon Gari da ke jihar. 

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bada bayanai a kan irin waɗannan lalatattun kayan, inda ya yi kira da a riqa duba bayanin kayan masarufi kafin a yi amfani da shi.