An gano musabbabin mutuwar tsohon shugaban Angola

Binciken farko da aka gudanar a Spain, ya nuna cewa, tsohon shugaban Angola, Jose Eduardo dos Santo ya yi mutuwar Allah ne, saɓanin zargin da ‘yarsa ta yi na cewa, kashe shi a aka yi.

Dos Santos wanda ya yi wa Angola mulkin kama-karya tsakanin 1979 zuwa 2017, ya mutu ne a ranar Juma’ar da ta gabata a wani asibiti da ke birnin Barcelona, inda ya tare tun a watan Afrilun 2019.

An kwantar da dos Santos mai shekaru 79 a sashin kula da marasa lafiya da ke cikin matsanancin hali a asibitin bayan ya gamu da bugun zuciya a ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata.

Daya daga cikin ‘ya’yansa mai suna, Welwitschia ce ta buƙaci a gudanar da bincike kan gawar mahaifinta domin gano ainihin musabbabin mutuwarsa, tana mai cewa, akwai lauje cikin naɗi a mutuwar tasa.

Sai dai binciken farko ya nuna cewa, marigayin ya yi mutuwar Allah ne bayan fama da bugun zuciya da kuma lalura a allon ƙirjinsa.

Majiyoyin sirri sun ce, za a sake zurfafa bincike game da mutuwar tasa.

Tuni dai ‘yar tasa ta shigar da ƙara a kotun Spain, tana zargin matar mahaifinta , Ana Paula da kuma likitansa da hannu a mutuwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *