Ƙasar Azerbaijan ta gayyaci Matawalle zuwa ziyarar aiki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan ƙasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya, Dr Bello Muhammad Matawalle, ya karɓi goron gayyatar girmamawa daga Jamhuriyar Azerbaijan domin gudanar da wata ziyarar diflomasiyya.

Ministan harkokin tsaron Azerbaijan, Mr Vugar Mustafayev, ne ya miƙa wannan gayyata a wani yunƙuri na arfafa dangantakar haɗin guiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin tsaro.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa Matawalle a fannin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar, manufar wannan ziyara ita ce tattaunawa kan haɗin guiwa a fannin ƙera kayan aikin samar da tsaro da kuma musayar fasahar soji.

A yayin ziyararsa zuwa Azerbaijan, Matawalle ya gudanar da wani muhimmin taro da shugabannin kamfanin Improteɗ Industries a babban birnin ƙasar, Baku, a ranar 17 ga Yuli, 2025.

An tarbe shi da girmamawa daga Shugaban kamfanin, Mr Fizuli Alakbarov, wanda ya kai Matawalle cikin masana’antar su ta zamani da ke ƙera kayan samar da tsaro.

Ministan ya duba wasu daga cikin manyan kayayyakin aikin soja na zamani da suka haɗa da na’urar tono bama-bamai (Mine Sweepers), motocin sojoji masu kariya na zamani (MRAPs), motocin kashe gobara, da kuma jiragen yaƙi marasa matuƙi (UAVs).

Kamfanin Improteɗ wanda aka kafa a shekarar 1991, ya zama ɗaya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke ƙera motocin yaƙi da sauran kayan tallafin rundunar soji a filin daga.

Wannan ziyara na da matuƙar muhimmanci wajen cika burin Nijeriya na sabunta masana’antar tsaronta ta hanyar haɗin guiwa da ƙasashen waje.

By ukarofi