Yadda manoman Nijeriya ke ƙaurace wa masara da shinkafa saboda tsadar taki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Manoman shinkafa da masara a Nijeriya na fargabar za su iya tafka asara sakamakon tsadar taki da sauran kayan aikin noma.

Wasu manoman kuwa sun haƙura da noman shinkafar kacokan sun koma noman wani abu daban, saboda a cewarsu tsadar taki ba za ta bari su samu riba ba.

Wannan dai na zuwa ne duk da iƙirarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ta rage farashin takin zamani ga manoma a sassan ƙasar don tallafawa harkokin noma.

Wani manomi a jihar Jigawa, Alh. Muhammad Idris ya shaida wa BBC cewa ya kashe kuɗi har naira miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas wajen sayen taki da zai yi noma da shi da kuma kuɗin banruwa a kowacce kadada.

“Duk da kuɗin da na kashe wajen noma, gaskiyar magana ita ce babu ribar da zan samu idan aka yi la’akari da tsadar taki da ya tashi da kuma shi kansa shinkafar, nawa ake sayar da ita yanzu?” inji Alh. Idris.

“Aƙalla, mafi ƙanƙanta na shinkafa idan aka noma a samu buhu daga 40 zuwa 60 a hecta, saboda haka idan mutum ya duba kuɗin da ya kashe, mutum zai ga babu wata riba.”

Rahotanni daga sassan Nijeriya na cewa wasu manoman sun daina noman masara da shinkafa inda suka koma noman gero da dawa da rogo da kuma riɗi gadan-gadan.

Alh. Idris ya kuma ce yana kira ga gwamnatin ƙasar ta duba harkar noma ta waiwaiyo kan manoma ta hanyar saka tallafi kan taki domin sun dinga siyansu cikin sauƙi da kuma samar musu da maganin ciyawa cikin sauƙi.

By ukarofi