Ƙasar Sin na taimakawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya

Daga CMG HAUSA

Yauzu haka, tattalin arzikin duniya na ci gaba da fuskantar matsin lambar da sauye-sauyen yanayin duniya da annobar COVID-19 suka haifar, lamarin da ya sa ake mai da hankali sosai kan yanayin raya tattalin arziki a ƙasar Sin, wadda ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ta ƙasashe da yankuna fiye da 120.

Matakan da ƙasar ta ɗauka wajen tinkarar annobar COVID-19 sun ba ta damar daƙile yaɗuwar cutar gami da raya ɓangaren samar da kayayyaki.

Kana yadda ƙasar take ƙoƙarin magance samun masu kamuwa da cutar COVID-19, ya sa ta iya kiyaye wani yanayin tattalin arziki da na zaman al’umma mai ƙarƙo, ba tare da salwantar da kuɗi da kayayyaki, da ƙarfin mutane ba.

Ban da haka, yadda ƙasar Sin take fitar da ƙarin kayayyaki zuwa kasuwannin ƙetare, ya sa kasashen yamma irinsu Amurka da Birtaniya ke iya gudanar da harkokinsu yadda suke buƙata.

Matakan hana yaɗuwar cutar COVID-19 da ƙasar Sin ta ɗauka suna taimakawa tabbatar da ingancin ayyukan samar da kayayyaki a ƙasar, ta yadda ƙasar ke samar da dimbin gudunmawa wajen biyan buƙatun ƙasashe daban daban na samun isassun kayayyaki masu alaka da kandagarkin yaɗuwar cuta, da masana’antu, da zaman rayuwar jama’a ta yau da kullum.

Wasu alƙaluman da ma’aikatar kasuwancin ƙasar Sin ta gabatar sun nuna cewa, ƙasashen Amurka da Japan da Koriya ta Kudu, da Jamus sun zuba mafi yawan jari ga ƙasar Sin.

Ta la’akari da muhimmiyar rawar da waɗannan ƙasashen ke takawa a fannin tattalin arzikin shiyyoyinsu, za a iya ganin tasirin tattalin arizkin Sin a duniya.

Haka zalika, a kwanan baya, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sanar da daga matsayin kuɗin Sin RMB cikin kuɗin ƙasashe daban daban da ake iya biyan bashin asusun da shi na SDR, daga kaso 10.92 zuwa kaso 12.28.

Wannan ma ya nuna yadda gamayyar ƙasa da ƙasa suke da cikakken imani kan tattalin arziki da kasuwar hada-hadar kuɗi na ƙasar Sin.

Fassarawar Bello Wang