Adalci shi ne tushen haɗin gwiwa

Daga BELLO WANG

Yau Litinin ne aka ƙaddamar da bikin makon tinkarar sauyin yanayi a nahiyar Afirka na wannan shekara ta 2022, a ƙasar Gabon.

Haƙiƙa batun sauyin yanayi na ƙara janyo hankalin jama’a, musamman ma ta yin la’akari da yadda ake samun abkuwar ƙarin nau’o’in bala’u daga Indallahi a wurare daban daban.

A shekarar da muke ciki, ƙasashe da dama dake nahiyar Afrika, irinsu Madagascar,da Mozambique, da Malawi, sun fuskanci raɗaɗin wani nau’i na bala’u.

Kana an gamu da matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa dake Najeriya, sai kuma jihohin Zinder, da Maradi, da Diffa a jamhuriyar Nijar.

A cewar Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya nahiyar Afirka, matsalar sauyin yanayin duniya, ta kan haddasa asarar dalar Amurka biliyan 7 zuwa 15 a ƙasashen Afirka, a duk shekara.

Don daidaita wannan matsala, ƙasashen duniya sun ƙuduri niyyar rage fitar da iska mai dumama yanayi, tare da ƙulla wasu yarjeniyoyi, inda aka tanadi cewa, ƙasashe masu sukuni da ƙasashe masu tasowa, za su ɗauki nauyin daidaita matsalar sauyin yanayi tare, sai dai ayyukan da za su ɗauki nauyin gudanarwa sun sha bamban.

Wato ya kamata ƙasashe masu sukuni su rage fitar da iska mai ɗumama yanayi, da samar da kuɗaɗe da fasahohi ga ƙasashe masu tasowa, yayin da ƙasashe masu tasowa ba dole ne a ƙayyade musu yawan iska mai ɗumama yanayi da za su riƙa fitarwa ba
Sai dai har zuwa yanzu, ba a aiwatar da waɗannan ƙa’idojin da kyau ba.

Maimakon haka, ƙasar Amurka da ƙasashen Turai, da sauran ƙasashe masu sukuni, suna neman ikon jagorantar ayyukan tinkarar sauyin yanayi a duniya, don neman danƙa wa ƙasashe masu tasowa nauyi na rage fitar da iskar dake dumama yanayi.

Kana sau da yawa, ƙasashe masu sukuni sun ƙasa cika alƙawarin da suka yi, na samar da a kalla dala biliyan 100 ga ƙasashe masu tasowa a duk shekara, don tallafa wa aikin tinkarar sauyin yanayi.

Haka zalika, ƙasar Amurka ta ɓullo da dabaru daban daban, ciki har da na siyasa, don neman shawo kan ɓangaren samar da kayayyaki masu alaka da rage fitar da iska mai ɗumama yanayi, yayin da ƙasashen Turai a nasu ɓangare, suna fakewa da batun tinkarar sauyin yanayi, wajen ɗaukar matakan kariyar ciniki.

Dukkansu sun fi karkata ga moriyar kai fiye da moriyar bai ɗaya ta ɗan Adam.

Haƙiƙa, babu adalci a matakan ƙasashen Turai da ƙasar Amurka.

Saboda tun kafin ƙasashe masu tasowa su fara raya masana’antu, ƙasashe masu sukuni na yammacin duniya, sun kwashe kimanin shekaru 200 suna ƙoƙarin raya masana’antu tare da fitar da iska mai guba.

Kana yanzu haka ƙasashe masu tasowa, suna fitar da iska mai dumama yanayi ne sakamakon gudanar da masana’antu na samar da ɗimbin kayayyakin da kasuwannin ƙasashe masu sukuni ke buƙata.

Ban da wannan kuma, ƙasashe masu tasowa, ba su da ƙarfin ɗaukar karin nauyin rage fitar da iska mai ɗumama yanayi.

Haka wannan batu yake, musamman ma a ƙasashen Afirka.

Kamar yadda wani shahararren masani mai suna Taling Rodrigue, dan kasar Kamaru, ya fada: galibin ƙasashen dake nahiyar Afirka na ƙoƙarin raya kayayyakin more rayuwa, da masana’antu, inda suke tinkarar ƙalubaloli da yawa, musamman ma a fannonin raya tattalin arziki, da ƙaruwar yawan al’umma.

Sai dai a lokaci guda suna zama ƙarƙashin tarnakin manufofin rage fitar da iska mai ɗumama yanayi, wadda ta kasance iri daya da ta ƙasashen yamma.

Wannan yanayi ya sa ƙasashen Afirka ƙasa sauke nauyin da aka ɗora musu na rage fitar da iskar dake ɗumama yanayi.

Ganin haka ya sa ƙasar Sin da sauran ƙasashe masu tasowa ke daga murya a wurare daban daban, don yin kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa da su ɓullo da tsarin aiki mai adalci, don tabbatar da tushen haɗin gwiwar ƙasashen daban daban, a fannin tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya.

Muna jiran ƙasashen duniya, musamman ma ƙasashe masu sukuni na yammacin duniya, da su amsa wannan kira.