Atiku ya tallafa wa ‘yan Kasuwar Kwari da miliyan N50

…yayin da Ibrahim Sekarau ya sauya sheƙa zuwa PDP

Daga BABANGIDA S GORA KANO.

Ɗantakarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya jajanta wa ‘yan kasuwar Kantin Kwari bisa ɓarnar da ruwan sama ya yi musu, tare da ba su tallafin naira milyan hamsin dan rage raɗaɗin asarar da suka yi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Wazirin Adamawan yake karɓar tsohon sanatan Kano ta Arewa, Malam Ibrahim shekarau daga Jam’iyyar NNPP ranar Litinin ɗin makon nan a gidansa da ke Mundubawa, Jihar kano.

Atiku ya ce, abin a tausaya ne iftila’in da sami ‘yan kasuwar na kwari, musamman kuma idan aka yi la’akari da yadda Kihar Kano ta ginu a kan kasuwanci.

Don haka ya ce babu makawa dole ne a tallafa masu do rage musu raɗaɗin asarar da suka tafka.

A hannu guda, Atiku Abubakar ya ce lallai samun shekarau cikin tafiyar PDP zai taimaka matuƙa wajen ƙara wa jam’iyyar ɗaukaka da nasara mai ɗorewa a lokacin zaɓe mai zuwa.

Sai dai ya ce wannan taro ba na kamfe ba ne a wannan lokaci, taro ne na zuwa karɓar Malam Ibrahim Shekarau zuwa Jam’iyyar PDP, amma kuma suna nan zuwa taron kamfe nan gaba da yardar Allah.

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron komawar Shekarau PDP sun haɗa da tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Alh. Namadi Sambo da Dino Melaye da Ambasada Aminu Wali da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Ahmad maƙarfi da sauransu.