Barci ya kwashe wasu matuƙan jirgin sama a sararin samaniya

Barci ya ɗauke wasu matukan jirgin sama biyu mallakin ƙasar Habasha a yayin da ya ke tsaka da balaguro a sararin samaniya.

Jirgin ƙirar Boeing 737 mai ɗauke da fasinjoji 154, ya tashi ne daga birnin Khartoum na Ƙasar Sudan zuwa birnin Addis Ababa na Habasha a farkon makon nan.

Masu tuƙinsu na sararin samaniya da nisan kafa 37,000 tsakaninsu da qasa, sai barci ya ɗauke su gabanin isowarsu filin jirgin saman Addis Ababa inda za su sauka.

Masu kula da tashi da kuma saukar jiragen sama a filin, sun yi ta ƙoƙarin ankarar da su cewa suna daf da wuce inda ya kamata su soma saukar da jirgin, amma masu tuqin jirgin ba su farga ba.

Daga ƙarshe dai matuƙan jirgin sun farga ne yayin da wata kararrawa ta jirgin da ke sarrafa kansa ta yi qara don ankarar da su, cewa sun wuce iyaka, sannan suka farka daga likimon da suka yi.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa, matuƙan sun samu damar sauko da jirgin a iyaka ta biyu ta inda ya kamata su saukar da jirgin bayan sun wuce iyaka ta farko.

Mutane da yawa ne suka riqa tofa albarkacin bakinsu daga ban mamaki da takaici, zuwa tausayi da alhini, la’akari da yadda matuƙa jiragen sama na kamfanin ke wahalar jigila babu isasshen hutu a aikinsu.

Wannan dai na zuwa ne bayan faruwar makamancin wannan lamari kamar yadda kafar watsa labarai da ABC 7 ta ruwaito yadda wasu matukan jirgi biyu suka bige da barci a watan Afrilu bayan tasowa da daga birnin New York na Amurka zuwa birnin Rome na Italiy ɗauke da fasinjoji kusan 250.

Rahotanni na cewa, wahalhalun jigilar jirage da ke janyo wa matuƙa jirgin sama gajiya na ɗaya daga cikin ƙalubalen da ake fuskanta a harkar sufurin jiragen sama musamman a nahiyyar Turai.