Ƙasar Sin ta fitar da rahoto game da yadda Amurka ke take haƙƙin ɗan Adam

Daga CRI HAUSA

Ofishin yaɗa labarai na majalisar gudanarwar ƙasar Sin, yau Litinin ya fitar da rahoton take haƙƙin ɗan Adam a Amurka a shekarar 2021.

Rahoton ya bayyana cewa, halin da ake ciki game da batun kare haƙƙin ɗan Adam a Amurka, wanda ke ƙunshe da munanan bayanai, ya ƙara taɓarɓarewa a shekarar 2021. Maguɗin siyasa ya haifar da ƙaruwar mutuwar mutune a sanadiyar annobar COVID-19, yayin da harbe-harben bindiga a ƙasar ya kai sabon matsayi.

Rahoton ya ƙara da cewa, tsarin demokuraɗiyyar ƙarya da ya kai ga take ‘yancin mutane na shiga harkokin siyasa da yadda masu damara ke take doka, ya sanya rayuwa ta yi matuƙar wahala ga baƙin haure da ‘yan gudun hijira a Amurka.

Rahoton ya kuma yi nuni da yadda ƙasar ta Amurka ke ci gaba da nuna wariya ga ƙananan ƙabilu, musamman mutanen da suka fito daga Asiya.

A cewar rahoton, ayyukan Amurka na ƙashin kai sun haifar da sabbin rikice-rikicen jin kai a duniya.

Fassarawa: Ibrahim