Ƙasar Sin ta yi kira ga ɓangarori daban-daban su sassauta halin da ake ciki a Ukraine ta hanyar yin shawarwari

Daga CRI HAUSA

Game da halin da ake ciki yanzu a ƙasar Ukraine, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya yi jawabi a wajen taron manema labarai da aka shirya yau Talata, inda ya ce, ƙasar Sin na sake kira ga ɓangarori masu ruwa da tsaki, da su nuna haƙuri, don sassauta halin da ake ciki, da daidaita saɓani ta hanyar yin shawarwari.

Da safiyar yau Talata, mamban majalisar gudanawar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya zanta da takwaransa na Amurka Antony Blinken ta waya, inda suka yi musanyar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi Ukraine, da makamashin nukiliya a zirin Koriya.

Game da hakan, Wang Wenbin ya ce, ƙasar Sin na maida hankali sosai kan sauyawar halin da ake ciki a Ukraine. Kuma matsayin ta dangane da batun ƙasar Ukraine bai sauya ba, wato ya kamata a mutunta kulawar duk wata ƙasa, kana, ya dace a kiyaye ƙa’idoji da manufofin kundin tsarin mulkin MDD.

Taɓarɓarewar halin da ake ciki a Ukraine, na da alaƙa sosai da jinkirin aiwatar da yarjejeniyar Minsk. Kuma ƙasar Sin za ta ci gaba da tuntuɓar ɓangarori daban-daban, bisa gaskiya da adalci.

Fassarawa: Murtala Zhang