Ƙasar Sin za ta ɗauki sabbin ‘yan sama jannati da za su dudanar da binciken sararin samaniya a nan gaba

Daga CMG HAUSA

Hukumar kula da binciken sararin samaniyar ƙasar Sin (CMSA), ta sanar a jiya Lahadi cewa, ƙasar za ta ɗauki sabbin ‘yan sama jannati 12 zuwa 14, waɗanda za su gudanar da ayyukan binciken sararin samaniya a nan gaba.

Daga cikin ‘yan sama jannatin da ke cikin shirin ko-ta-kwana, kana rukuni na huɗu na ‘yan sama jannatin ƙasar, bakwai zuwa takwas daga cikinsu za su kasance matuƙa kumbunan sama jannati, biyar zuwa shida daga cikinsu za su kasance injiniyoyin kumbunan sama jannati da ƙwararru masu kula da gwaje-gwaje, ciki har da guda biyu a matsayin ƙwararru masu kula da gwaje-gwaje, a cewar CMSA.

A cewar hukumar, za a ɗauki matuƙa kumbunan sama jannati ne daga cikin matuƙa dake aikin soja.

Za a zabo injiniyoyin kumbunan sama jannatin ne daga cikin waɗanda ke gudanar da ayyukan binciken kimiyya da aikin injiniyan sararin samaniya da sauran ɓangarori da abin ya shafa, yayin da ƙwararru masu kula da gwaje-gwaje, za su fito ne daga masu bincike dake dora muhimmanci kan kimiyyar sararin samaniya da dai sauransu.

A matsayinta na mai shirya daukar ma’aikatan, a karon farko hukumar CMSA, za ta zaɓo ƙwararru masu kula da gwaje-gwaje daga yankunan musamman na Hong Kong da Macao na ƙasar Sin.

A cewar CMSA, ana sa ran kammala ɗaukar sabbin ‘yan sama jannati ne a cikin shekara ɗaya da rabi.

Mai fassara: Ibrahim